Matar Aure Ta Biyewa Zuciya Ta Kashe Mijinta da Tabarya a Neja
- Wata matar aure ta yi aika-aika bayan ta sanya taɓarya ta rafke mijinta da ita a jihar Neja da ke yankin Arewa ta Tsakiya
- Matar auren mai suna Fatima Dzuma ta yi amfani da nauyin barcin mijinta wajen aika shi zuwa barzahu bayan sun samu saɓani
- Kakakin rundunar ƴan sandan Neja wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce wacce ake zargin tana hannun jami'an tsaro
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Neja - An cafke wata matar aure mai suna Fatima Dzuma bisa zargin kashe mijinta mai suna Baba Aliyu, a ƙauyen Lafiyagi Dzwafu da ke ƙaramar hukumar Katcha a jihar Neja.
Fatima Dzuma ta auri Baba ne shekara uku da suka wuce a matsayin matarsa ta biyu bayan ta rabu da mijinta na farko.

Source: Facebook
Matar aure ta kashe mijinta
Jaridar The Nation ta ce majiyoyi sun bayyana cewa marigayin da Fatima sun saba samun saɓani a tsakaninsu.
Sun bayyana cewa ko a ranar da za ta aikata wannan ɗanyen aikin sai da suka yi faɗa, inda Baba ya zane Fatima.
Da take amsa laifin ta, Fatima Dzuma ta ba da labarin cewa an samu saɓani a tsakanin su a wannan daren, kuma mijin nata ya yi mata duka, sannan ya bar gidan bayan hakan.
"Bayan ya dawo ya kwanta. Na yi amfani da igiya na ɗaure wuyansa, sai ya kasa kwancewa. Na buge shi da taɓarya sau uku, sau biyu a kansa, ɗaya kuma a hannunsa. Na yi amfani barcin da yake yi domin yana yin mai nauyi."
"Bayan na kashe shi sai na sanya shi a cikin tabarma, na jefa shi ta bayan katanga na ja shi zuwa cikin daji da ke bayan gida kafin na dawo na wanke jinin da ya fito daga jikinsa lokacin da na kashe shi."
- Fatima Dzuma
Meyasa ta kashe mijinta
Da aka tambaye ta dalilin da ya sa ta kashe shi, sai ta ce sun samu rashin fahimta ne, inda ta ce ba ta sonsa, sai ya lakaɗa mata duka.
A lokacin da ƴan uwan marigayin su ke nemansa, ta yi iƙirarin cewa ba ta gan shi ba amma daga baya ta amsa aikata laifin bayan kwanaki uku da ta kashe shi.
A cewarta, ita kaɗai ta aiwatar da kisan ba tare da taimakon kowa ba, rahoton Sahara Reporters ya tabbatar.
Ƴan sanda sun yi bayani kan lamarin
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Neja, DSP Abiodun Wasiu, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Kakakin ƴan sandan ya ce an gano gawar Baba Aliyu ne a wani daji da ke kusa da gidan, ya ce wacce ake zargin tana hannun ƴan sanda a halin yanzu.
Mutanen unguwa sun fafata da ƴan banga
A wani labarin kuma, kun ji cewa an ba hammata iska tsakanin ƴan banga da mutanen unguwa a jihar Neja, inda aka raunata mutum biyu.
Lamarin ya auku ne bayan jami'an tsaron na ƴan banga sun je kai farmaki kan wuraren da ake zargin mafakar ƴan daba ne da masu safarar miyagun ƙwayoyi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng


