Gwamna Ya Yabi Manufofin Tinubu, Ya Fadi Amfanin da Ya Samu
- Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya yaba da manufofin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan tattalin arziƙi
- Ya nuna cewa duk da akwai hauhawar farashin kayayyaki, a yanzu gwamnoni na samun kaso mai tsoka daga wajen gwamnatin tarayya
- Gwamna Abdulrazaq ya nuna cewa ayyukan da ya yi cikin shekara biyu na mulkin Tinubu sun fi waɗanda ya yi a shekara huɗun baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya yi magana kan manufofin tattalin arziƙi na gwamnatin Bola Tinubu.
Gwamna Abdulrazaq ya yabawa manufofin tattalin arziki na shugaba Bola Tinubu, inda ya ce sun inganta cigaban jihohi.
Gwamna Abdulrazaq ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a yayin ziyarar da gwamnoni suka kai wa shugaba Tinubu a Legas, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Abdulrazaq ya yabi manufofin Tinubu
Gwamna Abdulrazaq ya bayyana cewa a yanzu yana samun kuɗaɗe masu kauri daga gwamnatin tarayya, domin gudanar da ayyuka ga jama'a.
"Zan furta cewa ban yi shekara biyu a gwamnatin nan ba amma na yi ayyuka da yawa a cikin ƙasa da shekaru biyu fiye da na shekara huɗu a zangon farko."
"Hakan ya biyo bayan sauye-sauyen da kake yi. Sake fasalin tattalin arziki yana nufin muna samun ƙarin kuɗaɗe."
"Eh, akwai hauhawar farashin kayayyaki amma abin da muke samu ya zarce hauhawar farashin kayayyaki kuma muna yin abubuwa masu yawa."
"A yayin da wannan shekarar ta fara, na san tabbas za ka ziyarci jihohi da dama kuma za ka ga yadda sauyi ke gudana a jihohin, za ka yi alfahari da abubuwan da za ka gani."
- Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq
Manufofin gwamnatin Bola Tinubu na aiki
Gwamnan ya kuma yi nuni da nasarorin da aka samu a harkar noma a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, ya bayar da misali da yadda aka samu amfanin gona mai yawa a jihar Jigawa.
Ya ce hakan misali ne mai kyau na cewa manufofin gwamnatin Tinubu suna haifar da ɗa mai ido.
Shugaba Tinubu ya tura saƙo ga gwamnoni
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gayawa gwamnonin Najeriya manufarsa kan ƴancin cin gashin kan ƙananan hukumomi.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ko kaɗan bai da shirin ƙwace ƙananan hukumomi a hannun gwamnonin, face kawai yana son ya ga sun samu ci gaban da ya dace.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng