Hankula Sun Tashi bayan Jami'an Tsaro Sun Fafata da Mutanen Unguwa, An Gano Dalili

Hankula Sun Tashi bayan Jami'an Tsaro Sun Fafata da Mutanen Unguwa, An Gano Dalili

  • An samu tashin hankali a birnin Minna na jihar Neja bayan rikici ya ɓarke tsakanin ƴan banga da mutanen unguwa
  • Rikicin dai ya ɓarke ne a lokacin da ƴan bangan suka kai farmaki kan wasu wuraren da ake zargin maɓoyar masu aikata laifuka ne
  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce an kwantar da mutum biyu a asibiti waɗanda suka samu raunuka

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - An samu ɓarkewar rikici a tsakanin jami'an tsaro na ƴan banga da mutanen unguwa a jihar Neja.

Aƙalla mutane biyu da suka haɗa da ƴan banga ne aka kwantar a asibiti sakamakon rikicin da ya ɓarke a unguwar Soje da ke Minna, babban birnin jihar Neja.

'Yan banga sun fafata da mutanen unguwa a Neja
Mutanen sun yi gumurzu da 'yan banga a Neja Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ƴan banga sun yi rikici da mutanen unguwa

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa rikicin ya auku ne a ranar Talata da daddare.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun zo da sabon salon ta'addanci a Zamfara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin dai ya auku ne sakamakon farmakin da ƴan bangan suka kai a wuraren da ake zargin mafakar ƴan daba da masu safarar miyagun ƙwayoyi ne.

Mazauna unguwar sun bayyana cewa ɗaya daga cikin ƴan banga ya samu rauni a lokacin da suka yi arangamar.

Ɗaya daga cikin mazauna yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce wurin da aka kai farmakin, ba shi cikin daga cikin wuraren da ƴan daba ke samun mafaka.

Jami'an 'yan sanda sun yi bayani

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya ce an riga an umurci ƴan banga da su riƙa aiki tare da ƴan sanda a kodayaushe idan za su kai farmaki kan duk wani wurin da ake zargin akwai masu aikata laifuka.

"An kai waɗanda suka jikkata zuwa asibiti domin yi musu magani yayin da al’ummar yankin suka yi alƙawarin wanzar da zaman lafiya."

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke jami'in tsaro mai taimakon 'yan ta'addan Boko Haram

"Sai dai ana ci gaba da ƙoƙarin cafke waɗanda ake zargin da suka tsere, saboda ana gudanar da bincike kan laifin da ake zarginsu da aikatawa."

- SP Wasiu Abiodun

Jami'an DSS sun sheƙe ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an tsaro na hukumar DSS sun samu nasara kan miyagun ƴan bindiga a jihar Neja.

Jami'an na DSS waɗanda suka yi wa ƴan bindigan kwanton ɓauna, sun samu nasarar hallaka guda uku daga cikinsu har lahira.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng