Gwamna Zulum Ya Faranta Ran Ma'aikatan da Suka Yi Ritaya a Jihar Borno

Gwamna Zulum Ya Faranta Ran Ma'aikatan da Suka Yi Ritaya a Jihar Borno

  • Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya biya basussukan da masu karɓar fansho da giratuti suke bi
  • Babagana Umara Zulum ya amince da biyan N8bn na basussukan fansho da giratuti na shekarar 2019 zuwa 2021
  • Gwamna Zulum ya kuma ba da tabbacin cewa zai biya dukkanin basussukan giratuti kafin ƙarshen wa'adinsa a shekarar 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da biyan basussukan kuɗaɗen fansho da giratuti na ma'aikata.

Gwamna Zulum ya amince da biyan N8bn domin biyan bashin kudaden fansho da giratuti na malaman firamare da suka yi ritaya da sauran ma’aikatan da suka yi aiki da gwamnati.

Zulum ya biya basussukan fansho da giratuti
Gwamna Zulum ya ba da tabbacin biyan basussukan fansho da giratuti Hoto: @GovBorno
Asali: Twitter

Zulum ya sanar da amincewar ne a ranar Laraba a zauren majalisar zartaswar jihar da ke gidan gwamnati da ke Maiduguri, kamar yadda ya sanya a shafin X.

Kara karanta wannan

Gwamma Abba Kabir ya jero ayyukan ci gaba da zai wawo jihar Kano a 2025

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Zulum ya biya basussukan fansho da giratuti

Kuɗin N8bn da aka ware za su biya basussukan da aka biyo na daga shekarar 2019 zuwa 2021.

Gwamnan ya saki N3bn a watan Yuni da Satumba na 2019, domin ya biya ma’aikata 1,684 da suka bar aikin gwamnati tsakanin shekarar 2013 zuwa 2019.

Gwamna Zulum ya kuma fitar da sama da N12bn a shekarar 2020 ga ma'aikatan da suka yi ritaya a matakin jiha da ƙananan hukumomi tsakanin 2013 zuwa 2017.

Farfesa Zulum ya ba masu ritaya tabbaci

Gwamna Babagana Umara Zulum ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta biya basussukan giratuti da fansho kafin ƙarshen wa’adinsa a 2027.

"Tun da na karɓi ragamar mulki a shekarar 2019 zuwa yau, mun fitar da kusan N25bn domin biyan kuɗin giratuti ga waɗanda suka yi aiki da ƙananan hukumomi da gwamnatocin jihohi."
"In sha Allahu, zan biya duk wasu basussuka na giratuti kafin na bar ofis a shekarar 2027."

Kara karanta wannan

"Wahalarku ba za ta tafi a banza ba," Tinubu ya aika sakon 2025 ga 'yan Najeriya

- Gwamna Babagana Umara Zulum

Zulum ya yi kira ga gwamnatin Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya nuna damuwarsa kan rashin fara aikin gyaran madatsar ruwa ta Alau.

Gwamna Zulum ya buƙaci gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaba Bola Tinubu da ta waiwayi aikin gyaran madatsar ruwan domin damina ta kusa dawowa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng