Rarara Ya ba Tchiani Kwana 20 Ya Maida Mulkin Nijar ga Fararen Hula ko Ya Dauki Mataki
- Fitaccen mawakin siyasa a Najeriya, Dauda Kahuta Rarara ya ce zai fara amfani da baiwarsa don taimakon mutanen Nijar
- Ya bayyana takaicin yadda Janar Abdourahamane Tchiani ya jagoranci juyin mulkin da ya hambarar da mulkin farar hula a kasar
- Rarara ya bayar da wa'adin kwanaki 20 a mayar da mulki ga tsohon shugaba, Mohammed Bazoum ko a fara shirin sabon zabe
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Fitaccen mawakin siyasa a Arewacin Najeriya, Dauda Adamu Kahuta Rarara ya fusata da yadda har yanzu aka gaza mayar da mulki ga farar hula a Nijar.
A ranar 26 Yuli, 2023 ne sojoji su ka far wa gwamnatin Mohammed Bazoum, har aka yi juyin mulki tare da ci gaba da garkame hambararren shugaban kasar.
A tattaunawarsa da Legit, Dauda Kahuta Rarara ya zargi Shugaban sojin Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani da garkuwa da tsohon shugaba, Mohammed Bazoum.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka kuma ya zarge shi da garkuwa da mutanen Nijar, da ma kan shi, ganin yadda Rarara ya ce ba ya iya fita daga gidansa.
Zargin Rarara a kan Abdourahamane Tchiani
Shahararen mawakin siyasa, Dauda Kahuta Rarara ya zargi Janar Abdourahamane Tchiani kunnen kashi ga kiraye-kirayen dawo da mulki ga fararen hula.
Rarara ya kara da cecwa;
"Duk yadda za a lallaba mutumin nan, ya saki mutanen da ya yi garkuwa da su, ya ki sakinsu. Ya yi garkuwa da Bazoum, ya yi garkuwa da kan shi, ya shiga daki ya kulle.
"Yanzu duk sojojin da su ke mutuwa a Nijar da farar hula da mutanen da ake yi wa kwace, duk mutumin nan bai san abin da ake ciki ba, to wanda bai san abin da ake ciki ba, ta ya ya san abin da ke faruwa a wata kasa.?'
Matakin da Rarara zai dauka kan Tchiani
Babban mawakin ya bayyana cewa zai yi amfani da basirar da Allah SWT ya ba shi wajen wayar da kan mutanen Nijar a kan illolin Janar Tchinani gare su.
Ya ce;
"Idan mutumin nan saki 'yan Nijar ba, to ni kuma zan fara wayar da kan mutanen nan, lallai mutanen nan karyar da ya ke musu na ccewa ya na kaunar Nijar, kishin kasa ya ke yi, so ya ke ya taimakwa Nijar, to magana ce ta shifcin gizo."
Rarara ya jaddada cewa ba za su ci gaba da zuba idanu Janar Tchiani ya na garkame 'yan Nijar ba gaira ba dalili, kuma ya hana farar hula mulki.
Rarara ya saki zazzafar wakar yabon Tinubu
A baya kun j i cewa sabuwar wakar da mawaki Dauda Kahuta Rarara ya yi wa Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ba 'yan Najeriya da dama mamaki, duba da halin da ake ciki.
Wasu na ganin baitukan ba su zo a lokacin da ya dace ba, ganin irin halin da ake ciki, da kuma yadda rashin tsaro ya addabi shiyyar Arewacin kasar a yayin da ake neman sauki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng