Kashim Shettima Ya Hango Abin da 'Yan Najeriya Za Su Yi a 2025

Kashim Shettima Ya Hango Abin da 'Yan Najeriya Za Su Yi a 2025

  • Mataimakin shugaban ƙasan Najeriya ya kwantar da hankalin ƴan Najeriya yayin da aka shiga sabuwar shekarar 2025
  • Kashim Shettina ya ce nan ba da jimawa ba ƴan Najeriya za su fara murmushi domin tattalin arziƙin ƙasar nan ya fara farfaɗowa
  • Ya nuna cewa gwamnati na aiki tuƙuru tare da majalisar tarayya domin magance tarin ƙalubalen da ƙasar nan ke fuskanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya hango abin da ƴan Najeriya za su yi a shekarar 2025.

Kashim Shettima ya bayyana cewa ƴan Najeriya za su yi murmushi tare da samun cigaba a shekarar 2025, ganin yadda tattalin arziƙin ƙasar nan ya fara farfaɗowa.

Shettima ya hango mafita a 2025
Kashim Shettima ya ce 'yan Najeriya za su yi murmushi a 2025 Hoto: @stanleynkwocha
Asali: Twitter

Kashim Shettina ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban ƙasa bayan wata ziyara da ya kai wa Shugaba Bola Tinubu a Legas ranar Laraba, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke jami'in tsaro mai taimakon 'yan ta'addan Boko Haram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kashim Shettima ya faɗi lokacin samun canji

Mataimakin shugaban ƙasan ya bayyana cewa nan da ɗan lokaci kaɗan ƴan Najeriya, za su ga canji domin tattalin arziƙin ƙasar nan ya fara dawowa kan turba.

"Tattalin arziki ya fara farafaɗowa, kuma nan da makonni da watanni masu zuwa ƴan Najeriya za su fara murmushi."
"Muna aiki tare da majalisar tarayya domin samar da ingantattun hanyoyin magance ƙalubalen da muke fuskanta a ƙasa."
"Babu wata ƙasar da ta tsira daga guguwar taɓarɓarewar tattalin arziƙi a faɗin duniya.
"Rikicin da ke faruwa a Ukraine da sauran al'amuran duniya da dama suna yi mana illa saboda muna cikin al'ummar duniya."

- Kashim Shettima

Sai dai ya tabbatarwa ƴan Najeriya cewa ƙasar ta tsallake siraɗi kuma tana kan hanyar samun ci gaba mai ɗorewa.

Shettima ya yi wa Najeriya addu'a

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shƴgaban ƙasan Najeriya, Kashim Shettima, ya gudanar da aikin Umrah a ƙasa mai tsarki wato Saudiyya..

Kara karanta wannan

NLC ta gano abin da ya kamata gwamnati ta maida hankali a kai a 2025

Shettima ya kwaroro addu'o'in neman Allah Maɗaukakin Sarki ya ba shugabannin Najeriya ikon sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng