Tsadar Rayuwa: Ƴan Kwadago Sun Fara Neman Ƙarin Albashi Fiye da N70,000 a 2025

Tsadar Rayuwa: Ƴan Kwadago Sun Fara Neman Ƙarin Albashi Fiye da N70,000 a 2025

  • Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta TUC, Festus Osifo ya ce sun fara fafutukar dawo da ƙarin albashi duk shekara maimakon bayan shekara biyar
  • Osifo ya bayyana cewa ya kamata gwamnati ta riƙa zama tana ƙimanta mafi ƙarancin albashin ma'aikata bisa la'akari da farashin kaya duk shekara
  • Ya ce tuni suka fara wannan tattaunawar kuma tana ɗaya daga cikin batutuwan da za su tasa a gaba a sabuwar shekara 2025

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ƙungiyar kwadago ta kasa ta bayyana cewa za ta nemi a riƙa ƙara mafi karancin albashin da ake biyan ma'aikata duk shekara a Najeriya.

Ƙungiyar kwadagon ta ce yana da muhimmanci albashin da ake ba ma'aikata ya yi daidai da yanayin tsadar kayayyaki a ƙasar nan.

Shugaban TUC, Festus Osifo.
Yan kwadago sun sake ɗauko batun ƙarin albashin ma'aikata a 2025 Hoto: Festus Osifo
Asali: Facebook

Shugaban kungiyar kwadago ta TUC, Festus Osifo ne ya bayyana hakan a cikin shirin siyasa a yau na Channels tv rana Laraba, 1 ga watan Janairu, 2025.

Kara karanta wannan

"Ba za mu saurarawa gwamnati ba," ASUU ta fadi abin da ke kashe ilimi a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan kwadago za su nemi karin albashi a 2025

Ya ce maimakon bayan shekara biyar, ƴan kwadagon za su nemi gwamnati ta riƙa yi wa ma'aikata ƙarin albashi duk shekara duba da yanayin hauhawar farashin kaya.

"Abin da muka fara tunani shi ne, maimakon gwamnati ta jira shekaru biyar kafin ƙarin mafi ƙarancin albashi, me zai sa ba za a riƙa ƙarin albashin duk shekara ba?"

Kungiyoyin NLC da TUC sun fara tattaunawa

Shugaban TUC ya ce mambobin kungiyar da kuma takwarorinsu na kungiyar kwadago ta Najeriya watau NLC sun fara tattaunawa a kan haka.

“Alal misali, mun shiga Janairu 2025, zuwa ranar 15 ga watan, hukumar ƙididdiga ta ƙasa za ta fitar da alkaluman hauhawar farashin kayayyaki na watan Disambar 2024."
“Don haka abin da muke nema shi ne, idan alal misali hauhawar farashin kaya ya kai kashi 35%, a yi amfani da shi a mafi karancin albashi na ₦70,000, ta yadda za a ƙimanta albashi daidai da yanayin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Abin da Tinubu ya fadawa gwamnonin Najeriya a Lagos, ya ba su shawara

"Idan muka shiga shekara ta gaba 2026 a sake zama a yi kamar haka, wannan shi ne abin da muke fafutuka a kai, ba sai mun riƙa jiran bayan shekara biyar ba."

- Festus Osifo.

Yan kwadago za su sake miƙa buƙata a 2025

Shugaban TUC ya ce wannan wani bangare na cikin abubuwan da suka shirya tunkara a bana duk da sun fara tattaunawar a bara amma za a ci gaba a 2025.

A watan Yulin 2024, bayan kwashe tsawon watanni ana tattaunawa, gwamnatin tarayya da ƴan kwadago sun cimma matsaya kan sabon mafi karancin albashi na ₦70,000.

Wani ɗan kwadago a Najeriya, Salisu Ibrahim ya shaidawa Legit Hausa cewa ko ba a yi ƙari ba, akwai buƙatar sake duba tsarin aiwatar da dokar albashin N70,000.

Ma'aikacin gwamnatin ya ce ƙarin ba wani abu ba ne idan aka kwatanta da yanayin tsadar rayuwar da ake ciki a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Matatar man Najeriya ta fara aiki bayan ta Fatakwal, da yiwuwar fetur ya ƙara araha

"Ni ina ganin ko da shugabannin kwadago ba su nemi a yi kari ba, ya kamata su duba tsarin da ake kai yanzu haka a jihohi, manyan ma'aikata ba a masu wani ƙarin albashi ba.
"Ƙananan ma'aikata su suka amfana da sabon albashin N70,000 amma manya kuwa sai kaga N20,000 wani ma kasa da haka aka kara masa, ya kamata dai a sake duba lamarin," in ji shi.

2025: Kungiyar NLC ta ba gwamnatoci shawara

A wani rahoton, kun ji cewa ƙungiyar kwadago ta shawarci gwamnatoci na kowane mataki su maida hankali kan inganta walwalar al'umma a 2025.

NLC ta ce babu abin da ƴan Najeriya ke bukata a yanzu face sauƙin rayuwa ta yadda za su yi walwala da farin ciki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262