2025: Kungiyar NLC Ta Sake Tunkarar Shugaba Bola Tinubu kan Kudirin Haraji
- Kungiyar kwadago watau NLC ta buƙaci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya janye kudirin harajin da ke gaban Majalisar Tarayya
- A sakon barka da shiga sabuwar shekara, shugaban NLC, Joe Ajaero ya ce ya kamata gwamnati ta janye kudirin domin a sake zama a kansa
- Kwamred Ajaero ya kuma bukaci gwamnatoci tun daga matakin ƙasa zuwa kananan hukumomi su aiwatar da dokar sabon mafi ƙarancin albashi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta sake nanata kiranta ga gwamnatin tarayya ta janye kudirin sauya fasalin harajin da ake ta cece-kuce.
Shugaban NLC na ƙasa, Joe Ajaero ya bukaci Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta janye kudirin daga gaban Majalisar tarayya.
Kwamared Ajaero ya bayyana hakan ne a sakon barka da shigowa sabuwar shekara 2025 wanda NLC ta wallafa a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NLC ta sake tunkarar Bola Tinubu kan haraji
Joe Ajaero ya ce NLC na bukatar a janye kudirin ne saboda kare walwala da jin dadin ma'aikatan Najeriya.
Shugaban ƴan kwadagon ya bukaci gwamnatin Najeriya ta riƙa yin harkokinta a buɗe kuma ta faɗi gaskiya a duk wata mu'amalarta da talakawa.
Bugu da ƙari, ya yi kira ga gwamnati a dukkan matakai ta ba da fifiko wajen kawo sauƙi da walwala a rayuwar mutame musamman talakawa masu ƙaramin ƙarfi.
NLC ta buƙaci ta gyara alaƙarta da ma'aikata
Joe Ajaero ya ce:
“A kan haka ne mu ke sake kira ga gwamnatin tarayya da ta janye kudirin harajin da ta gabatar a gaban Majalisar Dokoki domin sake zaman kansa da dukkan masu ruwa da tsaki.
“Yayin da muka shiga 2025, muna kira ga gwamnati ta inganta alaka da ma'aikata ta hanyar ɗaukar tattaunawar neman maslaha da muhimmanci da mutunta yarjejeniya da kungiyoyin kwadago.
Shugaban NLC ya kara da jaddada bukatar gwamnatoci a dukkan matakai su aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 akalla daga farkon 2025.
Cire tallafin man fetur bai magance komai ba
Kun ji cewa ƴan kwadago sun kata kokawa kan matsin tattalin arzikin da aka shiga sakamakon cire tallafin man fetur.
Kungiyar NLC ta nanata cewa cire tallafin bai haifar da wani abu mai kyau ba sai jefa al'umma cikin ƙunci da tsadar rayuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng