Zanga Zanga Ta Barke kan Zargin Nada Sarki da Karfin Gwamnati
- Al’ummar Umuekwenu a karamar hukumar Udenu ta Jihar Enugu sun gudanar da zanga-zanga kan zargin nada basarake ba tare da yardarsu ba
- Kotun Jihar Enugu ta bayar da umarnin dakatar da kowane mataki na nadin basarake har sai an kammala sauraron karar da ke gabanta
- Shugabannin al’umma sun yi kira ga gwamnatin Jihar Enugu da ta mutunta umarnin kotu tare da dakatar da duk wani yunkuri na karya doka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Enugu - Al’ummar Umuekwenu da ke karamar hukumar Udenu ta Jihar Enugu sun nuna rashin amincewarsu da kokarin nada Cif Chinwe Eze a matsayin sabon basaraken yankin.
Mutanen yankin sun gudanar da zanga-zanga a babban ofishin karamar hukuma, suna masu zargin kwamishinan kananan hukumomi na jihar da keta umarnin kotu.
Vanguard ta wallafa cewa wata kotu ta bukaci a dakatar da duk wani mataki na nada basarake har sai an yanke hukunci kan shari’ar da ke gudana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zargin keta umarnin kotu wajen nadin Sarki
Masu zanga-zangar sun yi ikirarin cewa kwamishinan kananan hukumomi yana kokarin karya umarnin kotu domin nada Cif Chinwe Eze ba tare da gudanar da zabe ba.
Wani daga cikin shugabannin yankin, Hillary Onah, ya ce mutanen yankin sun rubuta wasiku zuwa ga gwamnatin jihar Enugu domin nuna rashin amincewarsu da abin.
Zanga-zanga kan nada basarake a Enugu
Masu zanga-zangar kin amincewa da nada basaraken sun rike takardu masu dauke da rubuce-rubucen nuna rashin amincewa da abin da suka kira kokarin karya doka.
Sun bayyana cewa sarautar yankin ba ta sayarwa ba ce, kuma suna bukatar a mutunta tsarin zabe ta hanyar bin doka da oda.
Kiran kan mutunta dokar kotu
Hillary Onah ya bayyana cewa matsalar nada basarake a Umuekwenu ta kai shekaru 17, kuma matsalar tana ci gaba ne saboda rashin bin ka’ida.
Ya yi kira ga gwamnati da ta mutunta dokar kotu tare da tabbatar da cewa al’ummar yankin sun gudanar da zaben basarake cikin gaskiya da adalci.
An bukaci karrama sarakunan Arewa
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Shehu Sani ya bukaci a karrama wasu sarakunan Arewa da suka yi gwagwarmaya a lokacin zuwan Turawa.
Sanata Shehu Sani ya ce Turawan mulkin mallaka sun daure sarakunan saboda sun bukaci ba 'yan Najeriya 'yanci a kan haka ya kamata a tuna da su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng