Tinubu zai Kafa Kamfani domin Rage Tsadar Abinci a 2025
- Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta kafa sabon kamfani a 2025 domin rage tsadar abinci da sauran kayayyaki
- Kamfanin zai yi hadin gwiwa da Bankin Masana'antu, BOI, da Hukumar Zuba Jarin Kasa, NSIA, domin tallafa wa matasa da mata
- Wani magidanci, Umar Bello ya bayyanawa Legit cewa za su yi farinciki idan gwamnati ta dauki matakin rage tsadar abinci a 2025
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayyana aniyar gwamnatin tarayya na saukaka rayuwar al’ummar Najeriya a sabuwar shekara.
Bola Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabin sabuwar shekarar da ya gabatar ga kasa, inda ya bayyana cewa sabon kamfani da za a kafa zai rage tsadar kayan abinci.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa shugaba Bola Tinubu ya bukaci hadin kan 'yan kasa wajen daura Najeriya a kan turba mai kyau.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu zai kafa kamfanin rage tsada
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa sabon kamfani zai fara aiki kafin karshen zangon farko na shekarar 2025.
Kamfanin zai yi aiki tare da manyan hukumomi kamar Bankin Masana'antu (BOI), Hukumar Zuba Jarin Kasa (NSIA), da Ma’aikatar Kudi.
A cewar Tinubu, wannan matakin zai karfafa tsarin bashi, musamman ga matasa da mata, da kuma tallafa wa ci gaban tattalin arzikin kasa.
Shirin taron matasa na shekarar 2025
Shugaba Tinubu ya kuma bayyana cewa taron matasa da ya yi alkawari bayan zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa zai fara a farkon watannin 2025.
Punch ta wallafa cewa Bola Tinubu ya ce gwamnati na kokarin rage hauhawar farashi daga kashi 34.6% zuwa kashi 15%, tare da bunkasa samar da abinci da magunguna a cikin gida.
Tinubu ya bukaci hadin kan 'yan Najeriya
Shugaban kasa ya yi kira ga 'yan Najeriya da su yi watsi da bambance-bambancen siyasa, kabila, ko addini domin cimma burin tattalin arziki.
"Muna kan turbar gina Najeriya mai kyau ga kowa. Kada mu bari wani bangare na al’umma ya karkatar da mu daga wannan tafiyar.”
- Bola Tinubu
Shugaban ya kara da cewa gwamnati za ta kara karfafa dabi’u da kishin kasa a karkashin wani shiri na musamman a 2025.
Legit ta tattauna da Umar Bello
Wani magidanci mai 'ya'ya uku, Umar Bello ya ce abin farinciki ne a samu saukin abinci kuma hakan zai kara farin jini ga Bola Tinubu.
Sai dai Umar Bello ya nuna shakku kan cewa ba lallai a cika alkawarin ba lura da yadda 'yan siyasa suke gaza cika alkawura a baya.
Gwamnan Bauchi ya yi martani ga Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi ya yi martani ga fadar shugaban kasa bayan zarginsa da yin barazana ga Bola Tinubu.
Sanata Bala Mohammed ya ce maganar da ya yi a kan kudirin haraji ba barazana ba ce kawai yana gargadi ne kan abin da zai iya faruwa idan kudirin ya tabbata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng