Gwamna Ya Gargadi Jami'an Gwamnati kan Shiga Siyasa a 2025, Ya Fadi Matakin Dauka
- Gwamnan jihar Adamawa ya bayyana inda akalar gwamnatinsa za ta karkata a sabuwar shekarar 2025
- Ahmadu Umaru Fintiri ya gargaɗi jami'an gwamnatinsa da raba hankulansa ta hanyar tsunduma cikin harkokin siyasa
- Gwamna Fintiri ya yi gargaɗin cewa ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen korar jami'in gwamnatin da ya samu yana siyasa a 2025
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Adamawa - Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya yi gargaɗi mai zafi ga mutanen da ya naɗa muƙamai a gwamnatinsa.
Gwamna Fintiri ya gargaɗi mutanen da ya ba muƙamai da su ajiye burinsu na siyasa a 2025 su maida hankali wajen gina jihar.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Gwamna Fintiri yayi gargaɗin ne a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a Yola, babban birnin jihar Adamawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Fintiri ya gargaɗi jami'an gwamnati
Ya bayyana cewa duk wanda ya kasa bin wannan umarni to ya sauka daga muƙaminsa, rahoton tashar AIT ya tabbatar.
Gwamna Fintiri ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta amince da duk wani abu da zai riƙa raba hankalin jami'an gwamnati ba wajen sauke nauyin da ke kansu.
Gwamnan ya tabbatar da cewa idan lokacin siyasa ya zo zai goyi bayan ɗan takarar da ya samu nasara, amma a yanzu ya kamata a maida hankali wajen yin abin da ya dace.
"Babu batun siyasa a ajandar da nake da ita ta 2025, magana ce ta yi wa jama'a aiki."
"Kuma idan kuna cikin wannan gwamnati, har yanzu ina gaya muku idan kuna da ra'ayin siyasa, ku yi watsi da shi. a yi wa mutane aiki."
"Idan kuna tunanin kuna cikin gaggawa, nima zan yi gaggawar raba ku da muƙamanku."
- Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri
Gwamnan Adamawa ya ƙirƙiro masarautu
A wani labarin kuma, kun ji cewa jihar Adamawa ta samu sababbin masarautu har guda bakwai waɗanda Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya ƙirƙiro.
Gwamna Fintiri ya nuna fatan cewa sababbin masarautun da ya ƙirƙiro za su ƙara samar da wuraren warware saɓani da kawo ci gaba a tsakanin al'umma.
Asali: Legit.ng