'Yan Bindiga Sun Zo da Sabon Salon Ta'addanci a Zamfara

'Yan Bindiga Sun Zo da Sabon Salon Ta'addanci a Zamfara

  • Wasu fasinjoji da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba sun faɗa hannun ƴan bindiga a jihar Zamfaran Najeriya
  • Ƴan bindigan ɗauke da makamai sun yi awon gaba da fasinjoji 10 bayan sun yi wa motarsu kwanton ɓauna a kan hanyar Shinkafi zuwa Gusau
  • Miyagun ƴan bindigan sun kuma bankawa motar da fasinjojin da suke ciki wuta bayan sun yi awon gaba da su zuwa cikin daji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Wasu ƴan bindiga sun yi awon gaba da fasinjoji tare da ƙona motar su a jihar Zamfara.

Ƴan bindigan sun sace fasinjojin ne bayan sun tare motarsu a ƙaramar hukumar Shinkafi da ke jihar Zamfara.

'Yan bindiga sun kai hari a Zamfara
'Yan bindiga sun sace fasinjoji a Zamfara Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Kwanar Jalab da ke gundumar Zungeru a ƙaramar hukumar Shinkafi.

Kara karanta wannan

Sojoji sun fafata da 'yan bindiga, an rasa rayukan jami'an tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka sace fasinjoji a Zamfara

Wani mazaunin garin Shinkafi, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ƴan bindigan sun yi wa motar kwanton ɓauna ne da misalin ƙarfe 8:00 na safiyar ranar Talata, yayin da take ɗauke da fasinjoji zuwa Shinkafi daga Gusau.

"Ƴan bindigan sun sace dukkanin fasinjojin da ke cikin motar kafin su ƙona ta. Muna zargin an sace mutane 10 ciki har da direban motar."
"Kafin faruwar lamarin, ƴan bindiga ba su taɓa ƙona wata mota ba bayan sun yi awon gaba da fasinjoji. Tabbas suna yin garkuwa da mutane a kan hanya, amma ba su taɓa ƙona mota ba."

- Wata majiya

Ƴan bindiga sun sa jama'a cikin firgici

Ɗaya daga cikin mazauna garin mai suna Sulaiman Shinkafi ya ce mahaifiyarsa ta gargaɗe shi da ka da ya dawo Shinkafi bayan samun labarin aukuwar lamarin.

"Ina Gusau lokacin da aka samu labarin faruwar lamarin, sai Hajiya ta kira ni a waya ta umarce ni da ka da na koma Shinkafi sai washe gari."

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun yi ruwan wuta kan 'yan ta'addan ISWAP sun sheke tsageru masu yawa

"Ban san ainihin adadin mutanen da ƴan bindigan suka sace ba amma muna zargin su 10 ne saboda galibi direbobi na daukar mutane 10 a cikin motar su ta Golf, saɓanin mutane shida da aka saba ɗauka."

- Sulaiman Shinkafi

Bello Turji ya ci gaba da kai hare-hare

A wani labarin kuma, kun ji cewa tantirin shugaban ƴan bindigan nan, Bello Turji, ya koma ruwa wajen kai hare-hare ga jama'a a jihar Zamfara.

Bello Turji ya dawo kai hare-haren ne duk da roƙon da shugabannin Fulani suka yi masa na ya tsagaita da tayar da rikici a jihohin Sokoto da Zamfara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng