Gwamna Ya Nada Sabon Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnati da Wasu Mukamai
- Gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji ya yi rabon muƙamai ciki har da na shugaban ma'aikatan fadar gwamnati
- Biodun Oyebanji ya ɗauko kwamishinan kasafin kuɗi, Mista Oyeniyi Adebayo, ya ba shi muƙamin shugaban ma'aikatan fadar gwamnati
- Gwamna Oyebanji ya kuma naɗa Tajudeen Akingbolu a matsayin sabon shugaban hukumar kula da sufuri ta jihar Ekiti
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ekiti - Gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya yi rabon muƙamai a gwamnatinsa.
Gwamna Biodun Oyebanji ya amince da naɗin Mista Oyeniyi Adebayo, a matsayin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar.

Source: Twitter
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Mista Yinka Oyebode, ya fitar a birnin Ado Ekiti ranar Talata, cewar rahoton jaridar The Punch.
Gwamnan Ekiti ya yi naɗe-naɗe
Oyeniyi Adebayo, wanda a halin yanzu shi ne kwamishinan kasafin kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziƙi, zai fara aikin shugaban ma’aikatan fadar gwamnati daga ranar 2 ga watan Janairu, 2025.
Oyebode ya bayyana cewa Gwamna Oyebanji ya kuma samar da ofishin ayyuka na musamman, wanda Prince Wole Ajakaiye zai jagoranta a matsayin mai ba da shawara na musamman.
A halin yanzu Prince Wole Ajakaiye shine darakta janar/mai ba da shawara na musamman kan SDGs.
"Ana sa ran Oyeniyi Adebayo zai kawo ƙwarewarsa a fannin kuɗi, gudanarwa da tsare-tsare wajen gudanar da ayyukan ofishin gwamna."
"Gwamnan ya kuma amince da naɗin Femi Ajayi a matsayin kwamishinan kasafin kuɗi da tsare-tsare na tattalin arziƙi."
"Hakazalika Gwamna Oyebanji ya kuma amince da naɗin Barista Tajudeen Akingbolu a matsayin shugaban hukumar sufuri ta jihar Ekiti."
- Yinka Oyebode
Gwamnan Ekiti ya amince da sabon albashi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya amince da sabon mafi ƙarancin albashin da zai riƙa biyan ma'aikata.
Gwamna Oyebanji ya amince da N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi, sannan ya ba ma'aikata a kowane mataki tabbacin cewa za su amfani da sabon tsarin.
Asali: Legit.ng
