Wuta Ta Kama a Ofishin Ƴan Sanda ba Zato ba Tsammani, Jami'ai da Ma'aikata Sun Tsere

Wuta Ta Kama a Ofishin Ƴan Sanda ba Zato ba Tsammani, Jami'ai da Ma'aikata Sun Tsere

  • An shiga tashin hankali da wata gobara ta kama a wani ɓangaren caji ofis na ƴan sanda da ke Okokomaiko a jihar Legas
  • An ruwaito cewa gobarar ta taso ne daga wata tanka da ke zuba man dizel a otal ɗin kusa da ofishin jami'an ƴan sandan
  • Wasu shaidu sun bayyana cewa ma'aikatan otal din da ƴan sanda sun yi takansu don gudun kada wutar ta rutsa da su a ciki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Lagos - Wata gobara da ta taso daga wata tankar mai ta kone wani sashe na ofishin ‘yan sanda da ke Okokomaiko a jihar Legas.

Rahotanni sun ce tankar ta kama da wuta ne a lokacin da take zuba man dizal a cikin tankin ajiyar wani otel da ke da katanga daya da ofishin jami’an ‘yan sanda.

Kara karanta wannan

Wani mutumi ya harbi abokinsa kan gardama a otal, yan sanda sun kai ɗauki

Taswirar jihar Legas.
Wuta ta kama a ofishin ƴan sanda a jihar Legas ana tsaka da man dizel Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Gobara ta kama a ofishin ƴan sanda

Daily Trust ta ce Lamarin dai ya haifar da turereniya da rige-rige yayin da dukkan ma’aikatan otal din da ‘yan sandan da ke aiki a caji ofis suka tsero daga ofishinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an ƴan sanda da ke aiki a caji ofis din da ma'aikatan otal sun yi ta kansu domin tsira da rayuwarsu gudun kada wutar ta rutsa da su.

An bayyana cewa wutar ta fara kamawa ne daga injin motar kuma cikin kankanin lokaci ta bazu zuwa babban tankin dakon mai na tankar.

Yadda gobara ta yaɗu daga tankar mai

Shaidu da lamarin ya faru a gabansu sun bayyana cewa gobarar ta bazu har zuwa ofishin ‘yan sanda kafin a kai agaji.

Wani ganau mai suna Tolupe ya bayyana cewa direban babbar motar ya tsere ya bar ta a wurin lokacin da gobarar ta tashi.

Ya kara da cewa "Mafi yawan 'yan sandan da ke aiki a sashin sun gudu daga wurin don tsira da raƴuwarsu."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bude wuta ana shirye shiryen jana'iza, an rasa rayuka

Har kawo yanzu dai babu wata sanarwa a hukumnce kuma ba a samu rahoton rasa rai ba sakamakon wannan iftila'in.

Gobara ta kama a kasuwar masaka

A wani labarin, kun ji cewa gobata ta lalata kayayyin miliyoyin Naira a kasuwar Masaka da ke yankin karamar hukumar Kauru a jihar Nasarawa.

Rahotanni sun nuna cewa gobatarar ta tashi ne da daddare kuma ta ƙone shagunan ƴan kasuwa da dama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262