Jami'ar Abuja Ta Samu Sabuwar Shugaba bayan An Dade Ana Takaddama
- Farfesa Aisha Maikudi ta zama sabuwar shugabar jami'ar Abuja (UniAbuja) wacce ke a birnin tarayyar Najeriya
- A ranar Talata, 31 ga watan Disamban 2024 majalisar gudanarwar jami'ar ta amince da naɗin Farfesa Aisha Maikudi
- Naɗin na ta ya kawo ƙarshen taƙaddamar da aka daɗe ana yi kan shugabancin jami'ar da aka sauyawa suna kwanaki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Majalisar gudanarwa ta jami’ar Abuja (UniAbuja) ƙarƙashin jagorancin AVM Saddiq Ismaila Kaita (mai ritaya) ta amince da naɗin Farfesa Aisha Sani Maikudi a matsayin shugabar jami’ar.
An sanar da naɗin na ta ne yayin babban taron majalisar gudanarwar jam'iar karo na 77 a ranar Talata.
Aisha Maikudi ta zama shugabar jami'ar Abuja
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa muƙaddashin daraktan yada labarai da hulda da jama'a na jami'ar, Dakta Habib Yakoob ya fitar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa naɗin wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Janairun 2025, na tsawon shekaru biyar ne wanda za a sake sabunta shi ba.
Dakta Habib Yakoob ya bayyana cewa Aisha Maikudi ta zama wacce ta kere sauran abokan takararta guda 10 bayan an yi musu tantancewa.
An yi taƙaddama kan shugabancin UniAbuja
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa surutun ya biyo bayan shirin nadin sabon shugaban jami'ar.
Tun da farko dai masu ruwa da tsaki sun zargi majalisar gudanarwar da shirin nada Aisha Maikudi, wacce aka yiwa zargin cewa ba ta da adadin shekarun da ake bukata domin a nata muƙamin.
Haka kuma shirin naɗin ya haifar da rarrabuwar kawuna tsakanin 'yan majalisar gudanarwar jami'ar, inda wasu daga ciki suka ƙi zuwa taron da majalisar ta kira dangane da naɗin.
An sauya sunan jami'ar Abuja
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta sauya sunan jami'ar Abuja (UniAbuja) zuwa sunan tsohon shugaban ƙasa.
Gwamnatin tarayya ta sauya sunan UniAbuja zuwa jami'ar Yakubu Gowon bayan an amince da hakan a taron majalisar zartaswa ta tarayya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng