"Tinubu na da Hali Irin na Sardauna," Ganduje Ya Hango Abin da Zai Faru a 2025

"Tinubu na da Hali Irin na Sardauna," Ganduje Ya Hango Abin da Zai Faru a 2025

  • Shugaban APC na kasa ya tabbatar wa ƴan Najeriya cewa za su samu saukin rayuwa da farin ciki a sabuwar shekarar da za a shiga
  • Abdullahi Umar Ganduje ya ce Bola Tinubu na da halin kirki da fatan ci gaban Najeriya irin na su Sardauna da Tafawa Balewa
  • Tsohon gwamnan Kano ya ce alamu sun nuna tsare-tsaren tattalin arzikin Bola Tinubu za su kara fito da sakamako mai kyau a 2025

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dr Abdullahi Ganduje, ya ce 'yan Najeriya za su yi farin ciki a sabuwar shekarar da za a shiga watau 2025.

Tsohon gwamnan jihar Kano ya tabbatarwa ƴan Najeriya cewa alamu sun nuna ranaku masu kyau na jin daɗi na tafe a sabuwar shekara.

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Jonathan ya soki El Rufa'i kan zargin kabilanci a gwamnatin Tinubu

Shugaban APC, Dr. Abdullahi Ganduje.
Shugaban APC, Ganduje ya ba yan Najeriya tabbacin samun saukin rayuwa a 2025 Hoto: @OfficialAPCNig
Asali: Twitter

Ganduje ya ba da wannan tabbacin ne a sakon barka da sabuwar shekara da hadiminsa, Cif Oliver Okpala ya fitar a Abuja, kamar yadda Punch ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje ya ce za a ji daɗi a 2025

A cewarsa, sauye-sauyen da Shugaba Bola Tinubu ya aiwatar a kasar nan sun fara haifar da sakamako mai kyau, kuma komai zai kara fitowa fili a sabuwar shekara.

"Ina tabbatar maku da cewa daga nan zuwa bikin kirismetin baɗi, tattalin arziki zai daidaita kuma ya inganta.
"Lokaci ne da za mu yi fata na gari ga ƙasarmu kamar yadda muka gani daga mazan jiya irinsu Abubakar Tafawa Balewa, Ahmadu Bello Sardauna, Dr Herbert Macaulay , Nnamdi Azikwe, Obafemi Awolowo da sauransu.
"Waɗannan mutane sun yi wa goben kasarmu aiki tare da fatan ci gaba, ba wai don babu kalubale a lokacinsu ba, sai dai suna da yaƙini kuma sun yi imani duk wata matsala za ta wuce.

Kara karanta wannan

"An samu tsaro a 2024," Gwamnan a Arewa ya yabawa Shugaban Kasa Tinubu

Bola Tinubu na da niyya mai kyau

Ganduje ya bayyana cewa Bola Tinubu na da kyakkyawar niyya da fata na gari irin nasu Sardauna da Tafawa Balewa.

"Wannan shi ne irin yakinin da Bola Tinubu ke da shi shiyasa yake samun ci gaba. Dukkanmu muna bukatar mu shiga 2025 da ƙafar dama kuma da yaƙinin haɗuwa da alherai," in ji shi.

Ganduje ya kwantar da hankulan ƴan Najeriya

A wani labarin, an ji cewa Ganduje ya kwantar da hankalin ƴan Najeriya kan shirin gwamnatin Najeriya karkashin Bola Ahmed Tinubu.

Shugaban APC na masa ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ba ta da nufin kuntatawa kowa face kawo sauki da walwala a fuskokin al'umma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262