DHQ Ta Fadi Adadin Shugabannin 'Yan Ta'addan da Sojoji Suka Kashe a 2024

DHQ Ta Fadi Adadin Shugabannin 'Yan Ta'addan da Sojoji Suka Kashe a 2024

  • Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta yi bayani kan nasarorin da dakarun sojoji suka samu kan ƴan ta'adda a shekarar 2024
  • Daraktan yaɗa labarai na DHQ, Manjo Janar Edward Buba ya bayyana cewa dakarun sojojin sun hallaka ƴan ta'adda 10,937
  • Buba ya kuma bayyana cewa sojojin masu aikin samar da tsaro a sassan daban-daban na ƙasar nan sun ceto mutane 7,063 da aka sace

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Dakarun sojojin Najeriya sun hallaka ƴan ta'adda 10,937, waɗanda suka haɗa da kwamandoji da jagororinsu sama da 1,000 tare da ceto mutane 7,063 da aka yi garkuwa da su a shekarar 2024.

Dakarun Sojojin sun kuma kama masu laifi 12,538, yayin da ƴan ta’adda 16,171 da iyalansu suka miƙa wuya.

DHQ ta ce sojoji sun kashe 'yan ta'adda
DHQ ta ce sojoji sun hallaka 'yan ta'adda sama da 10,000 a 2024 Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: UGC

Daraktan yaɗa labarai na hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ), Manjo-Janar Edward Buba, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin da yake bayyana nasarorin da sojoji suka samu a shekarar 2024, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Jami'ar Abuja ta samu sabuwar shugaba bayan an dade ana takaddama

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun kashe shugabannin ƴan ta'adda

Manjo Janar Edward Buba ya bayyana cewa daga cikin shugabannin ƴan ta'addan da aka kashe a 2024 akwai Dutse Mainasara Idda, Malam Saleh Umaru, Mohammed Amadu da Chinemerem (wanda aka fi sani da Bam Bam).

Sauran su ne Jeremiah Uzuoma (wanda aka fi sani da Escoba), Tochukwu Awo (wanda aka fi sani da Ojoto) da Egwuatu, da sauransu, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Dakarun Sojoji sun ƙwato tarin makamai

Ya ce sojojin sun kwato makamai 8,815, alburusai 228,004 daga hannun ƴan ta’addan a shekarar 2024.

Makaman da aka ƙwato sun haɗa da bindigogi ƙirar AK47 guda 4,332, bindigogi ƙirar gida guda 1,244, bindigogin Dane guda 838, manyan bindigogi guda 259, da makamai iri-iri guda 2,131.

Ya ce alburusai da aka ƙwato sun haɗa da harsasai 128,496 na musamman masu kaurin 7.62mm, harsasan NATO guda 45,445 masu kaurin 7.62mm, harsasai 5,103, da alburusai iri-iri guda 29,176.

Kara karanta wannan

Sojoji sun fafata da 'yan bindiga, an rasa rayukan jami'an tsaro

Sojoji sun ragargaji ƴan ta'addan ISWAP

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin sama na Operation Hadin Kai sun yi ruwan bama-bamai kan ƴan ta'addan ƙungiyar ISWAP a jihar Borno.

Dakarun sojojin sun samu nasarar hallaka mayaƙan na ƙungiyar ISWAP a farmakin da suka kai musu a maɓoyarsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng