Watan Azumin Ramadan Ya Gabato, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwa
- Sarkin Musulmi ya bukaci Musulman Najeriya su fara fita duba jinjirin watan Rajab na shekarar 1446H daga ranar Talata, 31 ga Disamba
- Shugaban kwamitin kula da harkokin Musulunci na fadar sarkin Musulmi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jihar Sakkwato
- Ya ce ranar Talata ta kama 29 ga watan Jumada Thani, 1446AH kuma ita ce ranar fara duba sabon wata a Musulunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto - Mai alfarma sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar ya buƙaci al'ummar Musulmi su fara duban jinjirin watan Rajab daga yau Talata, 31 ga watan Disamba 2024.
Sultan ya bukaci a fara duba jinjirin watan Rajab na shekarar 1446 bayan hijira a wata sanarwa da fadar sarkin Musulmi ta fitar a jihar Sakkwato ranar Litinin.
Jaridar Guardian ta tattaro cewa sanarwar na ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin harkokin addinin Musulunci na fadar sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Junaidu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rajab 1446AH: Sarkin Musulmi ya fitar da sanarwa
Sultan Sa'ad Abubakar ya ce ranar Talata, 31 ga watan Disamba, 2024 daidai da 29 ga watan Jumada As-Sani, 1446 AH, ita ce ranar fara duba jinjirin watan Rajab.
"Muna sanar da al’ummar Musulmi cewa ranar Talata 31 ga watan Disamba, daidai da 29 ga Jumada Thani 1446H, ita ce ranar da za a fara duba jinjirin watan Rajab na shekarar 1446 bayan hijira.
"Saboda haka ana bukatar musulmi su fara neman jinjirin watan Rajab a ranar Talata kuma su kai rahoton ganinsa ga hakimi ko magajin gari mafi kusa don tuntubar Sarkin Musulmi."
- Alhaji Sa'ad Abubakar.
Watan azumin Radamaan ya gabato
Sarkin Musulmi ya yi addu'ar Allah ya ƙara taimakon dukkan Musulmi yayin da suke ƙoƙarin yi masa biyayya da sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na ibada, in ji Aminiya.
Rajab shi ne wata na bakwai a kalandar Musulunci kuma yana ɗaya daga cikin watanni hudu masu tsarki a Musulunci waɗanda aka haramta yaki a cikinsu.
Watan dai da cikin alamun gabatowar watan Ramadan, wata na tara a kalandar Musulunci wanda Musulmai ke yin azumi a cikinsa.
Sarkin Musulmi ya ba Sakkwato shawara
A wani labarin, kun ji cewa sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar III ya bukaci jihar Sakkwato ta yi koyi da haɗin kan jihar Kebbi.
Ya ce irin yadda manyan shugabannin al'umma a jihar Kebbi suka haɗa kansu, da masu mulki da waɗanda suka gama suka sauka, abin koyi ne ga sauran jihohi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng