Wani Mutumi Ya Harbi Abokinsa kan Gardama a Otal, Yan Sanda Sun Kai Ɗauki
- Yan sanda sun kama wani mutumi da ya buɗewa abokinsa wuta kan wata gardama da ta shiga tsakaninsu a ɗakin otal a Abuja
- Kwamishinam rundunar ƴan sanda, CP Olatunji Rilwan Disu ya ce jami'ai sun kwato mugayen makamai daga gidan wanda ake zargi
- Ya ce matashin da aka harba na kwance yana jinya a asibiti yayin da suke shirin gurfanar da wanda ya aikata wannan ɗanyen aiki a kotu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Jami’an rundunar ‘yan sandan Abuja sun kama wani mai suna Obinna Nwigwe, dan shekara 33, bisa zargin ya bude wa abokinsa wuta suna tsakiyar gardama.
Kwamishinan ‘yan sandan Abuja, CP Olatunji Rilwan Disu, ne ya bayyana hakan da yake gabatar da wasu mutane da ake zargi a Abuja, ranar Talata.
Hakan na kunshe a wata sanarwa da hukumar ƴan sandan birnin tarayya Abuja ta wallafa a shafinta na X ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutumin da ya harbi abokinsa ya shiga hannu
Olatunji Disu ya ce mutumin ya harbi abokinsa ne a lokacin da wata gardama ta shiga tsakaninsu kan wani abu a ɗakin otal.
CP Disu ya bayyana cewa lamarin ya auku ranar 26 ga watan Disamba, 2023 a wani otal da ke cikin Abuja.
"Ƴan sanda sun samu kiran gaggawa daga otal na 'Najob Guest House' kuma daga isarsuwurin suka ci karo da wani matashi, Andrew Philemon ɗan shekara 29 yana zubar da jini.
"Jami'anmu sun tarar da matashin na zubar da jini sakamakon munanan raunuka a jikinsa."
Ƴan sanda sun kwato makamai a gidansa
CP Disu ya ƙara da cewa jami’an ‘yan sanda sun kama Nwigwe dauke da bindiga a wurin da lamarin ya faru, wanda ya sa suka bincike gidansa suka gano alburusai.
Ya ce makaman da suka fito daga gidan mutumin sun hada da bindigogin dane guda 5, AK-47 Magazines mai dauke da harsashi 29 da wasu miyagun makamai.
Disu ya ce a halin yanzu Philemon na kwance yana jinya a babban asibitin kasa da ke Abuja, yayin da Nwigwe kuma za a gurfanar da shi a kotu da zarar an kammala bincike.
Nasarorin ƴan sanda a Katsina a 2024
A wani labarin, kun ji cewa dakarun rundunar ƴan sanda reshen jihar Katsina sun yi nasarar daƙile ayyukan miyagu da dama a cikin shekarar 2024.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Aliyu Musa ya bayyana wasu nasarori da suka samu a tsawon shekara guda, ciki har da aika ƴan bindiga lahira.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng