Alkawuran da Gwamnatin Tinubu ta Kasa Cikawa kan Tattalin Arziki a 2024

Alkawuran da Gwamnatin Tinubu ta Kasa Cikawa kan Tattalin Arziki a 2024

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu, ta yi wa ƴan Najeriya alƙawura da dama a fannin tattalin arziƙi a shekarar 2024.

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Sai dai, yayin da shekarar 2024 ke zuwa ƙarshe, akwai muhimman alƙawuran tattalin arziƙi da gwamnatin tarayya ta yi waɗanda har yanzu ba a cika su ba.

Gwamnatin Tinubu ta gaza cika wasu alkawura
Gwamnatin Tinubu ba ta cika wasu alkawura ga 'yan Najeriya ba a 2024 Hoto: Godswill Obot Akpabio
Asali: Facebook

Alƙawuran da Bola Tinubu bai cika ba

Yawancin alƙawuran an yi su ne da nufin rage raɗaɗin da ƴan Najeriya suka tsinci kansu a ciki, cewar rahoton jaridar The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin manufofin gwamnatin da suka jefa ƴan Najeriya cikin raɗaɗi akwai cire tallafin mai a watan Mayun 2023 da kuma sakin Dala sakaka.

Ga wasu daga cikin alƙawura da gwamnatin tarayya amma har yanzu ba a cika su ba.

1. Cire haraji kan shigo da kayayyakin abinci

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta soki kudirin harajin gwamnatin Tinubu, ta ba da shawara

Ɗaya daga cikin alƙawuran tattalin arziƙi da aka fi magana a shekarar 2024 shine cire haraji kan kayayyakin abinci da ake shigowa da su domin sauƙaƙa hauhawar farashi.

A ranar 10 ga watan Yuli, gwamnatin tarayya ta sanar da dakatar da haraji kan shigo da kayayyakin abinci, a matsayin wani ɓangare na rage matsalar taɓarɓarewar tattalin arziƙi sakamakon hauhawar farashin kayayyaki.

Ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari ya ce za a buɗe kafar shigo da kayayyakin abinci irin su masara, shinkafa, alkama da wake na kwanaki 150 ba tare da haraji ba, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Sai dai, yayin da shekarar 2024 ta zo ƙarshe, har yanzu ba a cika wannan alƙawarin ba.

2. Cire VAT a kan kayayyakin magunguna

A ranar 28 ga watan Yuni, shugaba Bola Tinubu ya rattaɓa hannu kan dokar da ta kawo tsarin cire harajin VAT kan kayayyakin magunguna da ake shigowa da su.

Kara karanta wannan

NLC ta gano abin da ya kamata gwamnati ta maida hankali a kai a 2025

Muhammad Ali Pate, mai kula da harkokin kiwon lafiya da walwalar jama'a, ya ce an ba da umarnin ne domin farfaɗo da fannin kiwon lafiyar Najeriya da kuma ƙara yawan kayayyakin kiwon lafiya.

Sai dai, har yanzu farashin magunguna na da ɗan karen tsada, saboda har yanzu gwamnatin tarayya ba ta aiwatar da wannan dokar ba.

3. Rage hauhawar farashi zuwa 21%

A watan Janairu, gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya ce ana sa ran hauhawar farashin kayayyaki zai ragu a shekarar 2024, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Cardoso ya ce za a rage hauhawar farashin kayayyaki ya sauka zuwa kaso 21.4 kafin ƙarshen shekara.

Sai dai, a cewar hukumar NBS ya zuwa watan Nuwamba, hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya kai kaso 34.6% cikin 100% wanda shi ne mafi girma a cikin shekara 28.

4. Ƴancin cin gashin kai na ƙananan hukumomi

A ranar 11 ga Yuli, Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin cewa gwamnatin tarayya za ta iya tura kuɗaɗe kai tsaye ga asusun ƙananan hukumomi ba tare da sun bi ta hannun gwamnatocin jihohi ba.

Kara karanta wannan

Sojoji sun fafata da 'yan bindiga, an rasa rayukan jami'an tsaro

Kotun Ƙolin ta kuma umurci gwamnatin tarayya da ta riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomin da ba su da zaɓaɓɓun shugabanni.

Bayan watanni biyar, har yanzu gwamnatin tarayya ba ta aiwatar da ƴancin cin gashin kan ƙananan hukumomi ba ta fannin kuɗi kamar yadda Kotun Ƙoli ta tabbatar.

Tinubu ya yabawa kamfanin NNPCL

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna farin cikinsa kan fara aikin da matatar Warri da ke jihar Delta.

Mai girma Bola Tinubu ya yabawa kamfanin NNPCL bisa jajircewar da ya nuna wajen ganin cewa matatar ta dawo aiki kamar yadda ta saba a baya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng