An Fara Maganar Saukar Farashin Fetur bayan Farfado da Matatar Warri

An Fara Maganar Saukar Farashin Fetur bayan Farfado da Matatar Warri

  • 'Yan kasuwa da hukumar NMDPRA sun bayyana cewa farashin man fetur zai ci gaba da raguwa sakamakon fara aiki a matatar Warri
  • Ana hasashen cewa za a cigaba da samun gasa a tsakanin matatun man Najeriya wanda zai haifar da rage farashi domin samun kwastomomi
  • IPMAN ta yaba wa gwamnatin tarayya da NNPCL bisa nasarar da aka samu a Warri, ta kuma yi kira da a farfado da dukkan matatun Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - An fara fashin baki bayan fara aikin matatar man Warri mai iya tace gangar mai 125,000 a kullum, kamar yadda kamfanin NNPCL ya bayyana.

Masana da masu ruwa da tsaki a fannin sun nuna farin ciki da cewa ci gaban zai haifar da karin sauki ga al’umma ta fuskar farashi.

Kara karanta wannan

Yadda aka kashe 'yan bindiga 40, aka kama miyagu 916 a jihar Katsina

Matatar Warri
Matatar Warri za ta jawo rage farashin fetur. Hoto: NNPC Limited
Asali: Twitter

Punch ta rahoto cewa hukumar NMDPRA ta tabbatar da cewa farfadowar matatar Warri zai bunkasa gasa a kasuwa da rage dogaro da dala wajen shigo da kayayyaki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matatar Warri za ta rage farashin mai

Shugaban kula da ayyukan IPMAN, Mustapha Zarma ya bayyana cewa farashin mai zai ci gaba da sauka sakamakon kara yawan fetur da da ake tacewa a cikin gida Najeriya.

Daily Trust ta wallafa cewa 'yan kasuwar sun ce idan aka samu yawan kayayyaki a kasuwa, gasa za ta karu, kuma hakan zai rage farashi ga talakawa.

Haka zalika, shugaban NMDPRA, Ahmed Farouk ya ce fara aikin matatar Warri zai kawo karin nasara wajen tabbatar da samun saukin farashi a fadin kasar nan.

Bukatar samar da karin matatun mai

Shugaban NMDPRA, Ahmed Farouk ya ce farfado da matatun Warri da ta Port Harcourt abu ne mai kyau, kuma suna fatan matatar Kaduna ta biyo baya.

Kara karanta wannan

An kara karya farashin fetur, za a sayar da litar mai a N400

Haka nan, ya kara da cewa wasu masu zuba jari suna kafa matatun mai na zamani wadanda za su tallafa wa Najeriya wajen rage dogaro da shigo da kayayyakin mai.

Sakataren IPMAN na Abuja-Suleja, Mohammed Shuaibu, ya ce matatar Warri za ta taimaka wajen rage bukatar dala yayin shigo da mai daga kasashen waje.

Kwastam ta rage farashin mai zuwa N400

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar kwastam ta sanar da rage farashin man fetur domin rage radadin rayuwa ga al'umma.

Yayin wani taro a jihar Legas, kwastam ta bayyana cewa za ta sayar da litar man fetur mai yawa da ta kama a kan N400 yayin hidimar karshen shekara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng