Gwamna Ya Gano Wata Badaƙala, Ya Dakatar da Shugaban TSC da Wasu Ma'aikata

Gwamna Ya Gano Wata Badaƙala, Ya Dakatar da Shugaban TSC da Wasu Ma'aikata

  • Gwamnan Nasarawa ya dakatar da shugaban hukumar kula da harkokin malamau (TSC) da tawagarsa nan take
  • Abdullahi Sule ya ɗauki wannan matakin ne bayan gano wata badaƙala a ɗaukar sababbin malamai 1,000 da ya bayar da izini
  • Bayanai sun nuna cewa shugaban TSC da yan tawagarsa sun ɗauki malamai fiye da 1,000, sannan sun take dokar ɗaukar aiki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya dakatar da shugaba da mambobin hukumar kula da harkokin malamai ta jihar (TSC) nan take.

Gwamna Sule ya ɗauki wannan matakin ne bisa laifin take umarninsa wajen ɗaukar sababbin malaman makaranta 1,000.

Gwamna Abdullahi Sule.
Gwamnan Nasarawa ya dakatar da shugaban hukumar TSC da mambobin gudanarwa Hoto: Abdullahi A. Sule
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta tattaro cewa Abdullahi Sule ya kuma ba da umarnin gudanar da bincike mai zurfi kan wannan badaƙalar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin gwamna na ɗaukar wannan mataki

Kara karanta wannan

Malamai da ma'aikata sun jefa gwamna a matsala kan sabon albashin N70,000

Idan za ku iya tunawa a watan Fabrairu, 2023, Gwamna Sule ya sanar da shirin ɗaukar malamai 1,000 aiki domin cike giɓin ƙarancin malamai a Nasarawa.

An tattaro cewa hukumar TSC ta kara adadin duk da cewa ta gudanar da daukar ma’aikatan ba tare da bin doka da oda ba, ta ɗauki sama da malamai 1,000.

Laifin ya bayyana ne lokacin da hukumar TSC ta gaza biyan waɗanda ta ɗauka ta haramtacciyar hanya albashi duk da gwamna ya bada umarni.

Yadda TSC ta take umarnin Gwamna Sule

Malamai 1,000 da gwamna ya amince da ɗaukarsu aiki sun samu albashinsu yayin da ragowar da aka ɗauka ba bisa ƙa'ida ba suka ji shiru.

Hakan ya jawo ce-ce-ku-ce daga jama’a wanda ya sanya Gwamna Sule ya kira taron 'yan hukumar TSC da sauran jami’an ma’aikatar ilimi ta jihar Nasarawa.

Wadanda suka halarci taron sun hada da Kwamishinan Ilimi, Mista John Mamman da shugaban TSC, Malam Mohammed Gada.

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta ya ɗauki zafi, an kashe mutum 1 da faɗa ya kaure a wurin taro

Shugabannin TSC sun faɗawa gwamna gaskiya

A jawabansu a taron da ya gudanar a gidan gwamnati dake Lafia ranar Litinin, mambobin hukumar TSC sun amince da daukar malamai sama da 1,000 aiki ba tare da izini ba.

Bayan wuce gona da iri wajen ɗaukar adadin maƙaman, ana zargin hukumar ba ta bi tsarin da ya kamata ba, cewar rahoton Channels tv.

Don haka gwamnan ya bayar da umarnin a kafa kwamitin mutum uku da zai binciki badakalar bayan haka za a dauki matakin da ya dace.

Ma'aikata za su warwasa a Nasarawa

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Abdullahi Sule ya ba ma'aikatan gwamnati a Nasarawa tabbacin cewa za a masu karin albashi a watan Disamba.

Abdullahi Sule ya ce gwamnatinsa za ta fara aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na N70,500 da ta amince da shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262