Hatsarin Mota Ya Ritsa da Tawagar Gwamna, an Samu Asarar Rai

Hatsarin Mota Ya Ritsa da Tawagar Gwamna, an Samu Asarar Rai

  • Wani hatsarin mota ya ritsa da tawagar motocin gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia a ranar Lahadi, 29 ga watan Disamban 2024
  • Mazauna yankin da lamarin ya auku sun bayyana cewa mutum ɗaya ya rasa ransa sakamakon hatsarin motan da ya auku
  • Sai dai, wani hadimin gwamnan ya musanta cewa ayarin motocin sun yi hatsari wanda ya jawo kisan wani mutum

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Tawagar motocin gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia ta yi hatsari.

Rahotanni sun bayyana cewa mutum ɗaya ya mutu a wani hatsarin da ya ritsa da tawagar Gwamna Hyacinth Alia a garin Ihugh da ke ƙaramar hukumar Vandeikya a jihar Benue.

Hatsari ya ritsa da tawagar gwamnan Benue
Hadimin Gwamna Alia ya musanta aukuwar hatsari a ayarin motocin gwamnan Hoto: Fr. Hyacinth Iormem Alia
Asali: Twitter

Ayarin motocin Gwamna Alia sun yi hatsari

Mazauna yankin sun shaidawa jaridar Daily Trust cewa, haɗurran guda biyu sun auku ne a ranar Lahadi a kusa da kasuwar Ihugh da ke Vandeikya, mahaifar Gwamna Alia.

Kara karanta wannan

Gwamna ya faɗi yadda mahaifiya da ɗansa suka rasu bayan ya aurar da ɗiyarsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun bayyana cewa hatsarin na farko ya faru ne a lokacin da gwamnan ya je garinsu domin gudanar da bukukuwan Kirsimeti, inda wata mota a cikin ayarin motocinsa ake zargin ta kashe wani mutum.

Sun ƙara da cewa a hanyar komawa Makurdi, wani hatsarin ya ritsa da wata mota a cikin ayarin motocin gwamnan a Ihugh, inda wasu mutane suka jikkata.

Hadimin gwamna ya musanta lamarin

Sai dai Solomon Iorpev, mai ba Gwamna Alia shawara kan harkokin yaɗa labarai, ya musanta cewa hatsari ya ritsa da ayarin motocin gwamnan, inda ya jaddada cewa babu wanda ya mutu.

"Tawagar Gwamna Alia ba ta kashe kowa ba. Tuni ayarin motocinsa suka tafi coci. Abin da ya faru ya ritsa da wata mota da aka tura yin wani abu, lokacin da take kan hanyar dawowa."
"Ba ta a cikin ayarin motocin. Mota ɗaya ce kawai. Babu wani hatsari da ya ritsa da ayarin motocin."

Kara karanta wannan

Direba ya sha giya ya afka gidan mutane, ya jawo gobara a gidaje

"Misali, akwai motoci 17 a tawagar gwamnan, kuma kusan guda 15 suna gaba. Ɗaya daga cikinsu da aka tura wani waje tana kan dawowa sai ta yi hatsari."
"Shin wannan ayarin motoci ne? Hatsarin ma da daddare ya auku saboda ƙura a hanyar sannan direban bai ga wata mota da take tahowa a gabansa ba. Abin da ya faru kenan."

- Solomon Iorpev

Gwamnan Benue ya ba da hutu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia ya ba da hutu ga ma'aikata domin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.

Gwamna Hyacinth Alia ya buƙaci ma'aikatan da su yi amfani da lokacin hutun da ya ba da wajen komawa gona domin samar da wadataccen abinci a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng