Rikicin Sarauta Ya Ɗauki Zafi, An Kashe Mutum 1 da Faɗa Ya Kaure a Wurin Taro
- Mutum ɗaya ya mutu da rikicin da ya ɓarke kan sarauta a hedkwatar ƙaramar hukumar Ndokwa ta Gabas a jihar Delta
- Shugaban ƙaramar hukumar ya sanya dokar zaman gida daga karfe 7:00 na dare zuwa karfe 6:00 na safiya a garin Abuh bayan faruwar lamarin
- Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan Delta, Bright Edafe ya ce faɗan ya kaure ne a wurin taron rawar wanda aka ba sarauta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Delta - Rikicin naɗin sarauta a garin Aboh, hedkwatar karamar hukumar Ndokwa ta Gabas a jihar Delta ya ɗauki sabon salo.
Wani faɗa da ya kaure kan sarautar ya yi ajalin mutum ɗaya, wasu ƙarin mutane uku sun ji munanan raunuka a Aboh.
Rikicin sarauta: An kashe mutum 1 a jihar Delta
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa faɗa ya kaure tsakanin ɓangarori biyu masu adawa da juna a wurin wani taro da aka shirya wanda ya shafi sarautar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har yanzu dai babu tabbacin abin da ya haddasa faɗan a wurin taron amma wasu majiyoyi sun ce lamarin da ya fara daga wata yar gardama.
Lamarin dai wanda ya kai ga rasa ran mutum guda ya haifar da tashin hankali da zaman ɗar-ɗar a tsakanin mutanen garin.
An sa dokar kulle a jihar Delta
Shugaban ƙaramar hukumar Ndokwa ta Gabas, Mr. Vincent Osilonya ya sanya dokar zaman gida daga karfe 7:00 na dare zuwa 6:00 na safe a garin Aboh.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Delta, Mista Bright Edafe ya ce mutumin ya cika ne a asibiti.
Yan sanda sun faɗi yadda lamarin ya faru
"Mutum ɗaya ya mutu sakamakon faɗan ɓangarori biyu. An ba wani sarauta, to a al'ada idan aka ba mutum wannan sarauta sai ya yi rawa a gaban jama'a.
"Yana cikin rawa sai ya je har wurin da ƴan ɓangaren da suke adawa da shi ke zaune, su kuma suka farmake shi, waɗanda ke tare da shi suka tare masa, aka kama faɗa."
“Ana cikin haka ne aka fara harbe-harbe, mutum daya ya mutu yayin da wasu mutane uku suka samu raunuka daban-daban, an kai su asibiti domin yi musu magani."
- Bright Edafe.
Jami'an tsaro sun manaye fadar Ilesa
A wani rahoton, kun ji cewa dakarun ƴan sanda da wasu jami'ai sun mamaye fadar Ilesa bayan sanar da sabon sarki.
Clement Adesuyi Haastrup, tsohon mataimakin gwamnan Osun, shi ne aka zaɓa a matsayin sabon Owa-Obokun na Ijesa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng