Gwamna Ya yi Zarra, Ya Gabatar da Sama da Naira Tiriliyan 1 a Kasafin 2025
- Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 mai taken kasafin hadin kai da cigaba
- Rahotanni sun nuna cewa kasafin kuɗin ya fi na shekarar 2024 wanda ya kasance da kadan ya haura Naira biliyan 800
- Jimillar kuɗin da aka ware sun haɗa da Naira biliyan 462 domin ayyukan yau da kullum da Naira Biliyan 678 domin manyan ayyuka
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Rivers - Gwamnan jihar Rivers, Sir Siminalayi Fubara ya gabatar da kasafin kuɗin 2025 ga majalisar dokokin jihar karkashin jagorancin Rt. Hon. Victor Oko-Jumbo.
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa kasafin ya kai jimillar Naira tiriliyan 1.188, wanda ya zarce kasafin bara da Naira biliyan 388.

Source: Facebook
Legit ta tattaro rahoto kan yadda aka gabatar da kasafin ne a cikin wani sako da gwamna Fubara ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya bayyana cewa kasafin zai mayar da hankali kan tsare-tsaren ci gaba domin inganta rayuwar al’ummar jihar ta hanyar inganta tattalin arziki.
Wasu abubuwan da kasafin kuɗin ya kunsa
Yayin da yake gabatar da kasafin kuɗin, Gwamna Fubara ya ce jimillar kuɗin da ake fatan samu da kashewa a shekarar 2025 sun kai Naira tiriliyan 1.188.
Gwamna Fubara ya ce ayyukan yau da kullum da manyan ayyuka sun samu kashi 44:56%, wanda ke nuni da jajircewarsa wajen kawo abubuwan more rayuwa da cigaba a jihar.
Manufar kasafin kuɗin rivers na 2025
Gwamna Fubara ya bayyana cewa manufar kasafin ita ce tabbatar da ci gaban tattalin arzikin jihar da rage tasirin matsalolin tattalin arzikin ƙasa.
Ya kara da cewa kasafin yana ɗauke da dabarun da za su ƙarfafa jihar wajen jure matsalolin da tattalin arzikin ƙasa ka iya kawo wa.
Gwamnan ya kuma yaba wa majalisar dokokin jihar bisa goyon bayanta inda ya ce yana da matuƙar muhimmanci wajen cimma muradun kasafin kuɗi.
Gwamna Bago ya gabatar da kasafin N1.5tn
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Neja ya gabatar da kasafin kudin sama da Naira triliyan 1.
Gwamna Umaru Bago ya bayyana cewa kasafin zai bunkasa tattalin arzikin jihar Neja a shekarar 2025 tare da kawo walwala ga al'umma.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

