Gwamna Ya Faɗi Yadda Mahaifiya da Ɗansa Suka Rasu bayan Ya Aurar da Ɗiyarsa

Gwamna Ya Faɗi Yadda Mahaifiya da Ɗansa Suka Rasu bayan Ya Aurar da Ɗiyarsa

  • Gwamna Umar Namadi a jihar Jigawa ya tuna yadda mahaifiyarsa da ɗansa suka rasu mako guda bayan ya aurar da ɗiyarsa
  • Namadi ya godewa gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya bisa halartar bikin ɗiyarsa kuma ya sake dawowa ya masa ta'aziyya har gida
  • Gwamna Inuwa ya jagoranci tawaga zuwa gidan gwamnan a Kafin Hausa a Jigawa domin yin ta'aziyya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jigawa - Gwamnan Jigawa, Umar Namadi, ya bayyana cewa dansa, Abdulwahab, da mahaifiyarsa, Hajiya Maryam, sun rasu kimanin mako guda bayan da ya aurar da diyarsa.

Ɗan gwamnan ya rasu ne a makon da ya gabata a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi bayan sa’o’i 24 da rasuwar mahaifiyarsa.

Umar Namadi.
Gwamnan Jigawa ya faɗi yadda mahaifiyarsa da ɗansa suka rasu mako guda bayan aurar da 'yarsa Hoto: Umar Namadi
Asali: Twitter

Punch ta ce jiya Lahadi, gwamnan Gombe kuma shugaban gwamnonin jihohin Arewa, Inuwa Yahaya, ya jagoranci tawaga suka kai ziyarar jaje ga Namadi.

Kara karanta wannan

Gwamnan Bauchi ya yi ta'aziyyar iyalan takwaransa na Jigawa, ya yi addu'a

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Namadi ya faɗi yadda ya rasa mutum 2

Da yake jawabi lokacin da ya karɓi bakunci tawagar a Kafin Hausa da ke Jigawa, Gwamna Namadi ya godewa takwaransa na Gombe bisa nuna ana tare a lokacin farin ciki da alhini.

Ɗanmodi ya bayyana cewa Gwamna Inuwa ya halarci bikin ɗiyarsa, mako guda gabanin rasuwar mahaifiyarsa da kuma ɗansa.

“Mai girma gwamna, ka halarci ɗaurin daurin auren ‘yata a makon da ya gabata, yanzu kuma ka zo nan don jajanta mana bisa rasuwar mahaifiyata da kuma ɗana.
"Wannan ya nuna son da ka ke yi mana da kuma jagoranci na gari, ba mu da kalmar da za mu iya gode maka mai girma gwamna," in ji Namadi.

Gwamnan Gombe ya je ta'aziyya a Jigawa

Tun farko dai Gwamna Inuwa Yahaya ya roki Namadi da ya yi haƙuri ya miƙa lamarinsa ga Allah, inda ya ce rashin uwa da ɗa ba ƙaramar jarabawa ba ce.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban Majalisar Dattawa ya ziyarci gwamna domin yi masa ta'aziyya

A madadin gwamnonin Arewa da gwamnatin jihar Gombe, Inuwa Ya miƙa ta'aziyya ga Gwamna Namadi da al'ummar Jigawa bisa wannan rashi.

Ta'aziyyar gwamnan Bauchi, Bala Mohammed

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan gwamnan jihar Jigawa.

Gwamna Bala, shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP ya yi addu'ar Allah ya jiƙan mahaifiyar Umar Namadi da ɗansa, ya sa su a gidan Aljanna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262