Sanata Ali Ndume Ya ba Matasa Mafita kan Tsadar Rayuwa

Sanata Ali Ndume Ya ba Matasa Mafita kan Tsadar Rayuwa

  • Sanata Ali Ndume wanda ke wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa ya jawo hankalin matasa kan tsadar rayuwa
  • Ali Ndume ya buƙaci matasa su rungumi noma da kasuwanci a matsayin mafita kan tsadar rayuwar da ake fama da ita
  • Sanatan ya nuna cewa a yanzu lokaci ya wuce da za a tsaya ana dogara da gwamnati ko jiran albashi a ƙarshen wata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattijawa, Ali Ndume, ya ba matasa da al'ummar yankin shawara kan tsadar rayuwa.

Sanata Ndume ya buƙaci matasa da al’ummar yankin su rungumi harkar noma da kasuwanci domin shawo kan matsalar ƙarancin abinci da tsadar rayuwa.

Ndume ya ba matasa shawara
Sanata Ali Ndume ya bukaci matasa su rungumi noma Hoto: Sen. Mohammed Ali Ndume
Asali: Twitter

Sanatan ya bayyana haka ne a karshen makon da ya gabata a ƙananan hukumomin Gwoza da Askira Uba, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

Tchiani: An samu bayanai daga kasar waje kan zargin Najeriya da hada kai da Faransa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ndume dai yana yin ziyarar ƙarshen shekara ne a ƙananan hukumomi tara da kuma masarautu biyar na yankin Kudancin Borno.

Wace shawara Ali Ndume ya ba matasa?

Sanata Ndume ya bayyana cewa yadda ake samun taɓarɓarewar tattalin arziƙin duniya, mafita ɗaya daga yunwa shi ne mutane su yi noma mai yawa fiye da dogaro da gwamnati da albashi.

Ya ce mafi ƙarancin albashi na N70,000 a halin yanzu ba zai iya sayen buhun shinkafa ba wanda ya kai sama da N100,000, da buhun wake wanda ya kai N200,000.

Ya tunatar da jama’a cewa, kafin zuwan wannan gwamnatin, ana sayar da litar man fetur a kan Naira 200, amma ta haura zuwa Naira 1200, yayin da farashin dalar Amurka yake a Naira 600, a yanzu ya kai Naira 1600.

Bisa hakan sai ya yi kira ga jama’a da su rungumi noma da kasuwanci domin shawo kan matsalar taɓarɓarewar tattalin arziƙi.

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Jonathan ya soki El Rufa'i kan zargin kabilanci a gwamnatin Tinubu

Yadda Saraki ya ci amanar Ndume

A wani labarin kuma, kun ji Sanata Ali Ndume ya bayyana yadda tsohon shugaban majalisar dattawa ya yi masa yankan baya duk da goyon bayan da ya ba shi.

Sanata Ndume ya bayyana cewa duk da tsayawa tsayin daka kan Bukola Saraki, sai da aka dakatar da shi na wata takwas ba tare da albashi ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng