Gwamnan Bauchi Ya Shirya Liyafa ga Abokansa da Suka Yi Yarinta a Firamare

Gwamnan Bauchi Ya Shirya Liyafa ga Abokansa da Suka Yi Yarinta a Firamare

  • Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya shirya liyafa ga abokan karatunsa na shekarar 1971 a gidansa
  • Taron ya kasance mai cike da raha da kuma tattaunawar tunawa da rayuwar yarinta da yadda suke karatu a shekarun baya
  • Gwamna Bala Mohammed ya bayyana jin daɗinsa game da ƙaƙƙarfan alaƙar abota da suka kafa tun a lokacin yarinta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya shirya liyafa ta musamman domin karɓar abokan karatunsa na 1971 a gidansa.

Taron ya kasance mai cike da farin ciki, inda suka yi hira game da ƙwarewar da suka samu a lokacin yarinta da kuma yadda rayuwa ta tafi tun daga wancan lokaci har zuwa yau.

Kara karanta wannan

"An samu tsaro a 2024," Gwamnan a Arewa ya yabawa Shugaban Kasa Tinubu

Bala Muhammad
Gwamnan Bauchi ya gana da abokansa na firamare. Hoto: Senator Bala Abdulkadir Mohammed
Asali: Facebook

Legit ta gano yadda taron ya gudana ne a cikin wani sako da gwamna Bala Mohammed ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abokan karatun gwamna sun yi murnar haɗuwa

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana jin daɗinsa game da wannan haɗuwa da abokan karatunsa na 1971, inda suka tattauna game da abubuwan da suka faru a baya.

Sanata Bala Mohammed ya ce;

“Wannan rana ta kasance wata dama ta musamman wacce ta nuna muhimmancin dangantakar da muka kafa tun yarinta,
Alakar da muka kulla a baya ta cigaba da kasancewa wani muhimmin ɓangare na rayuwata.”

Muhimmancin abokanta da haɗin kai

Gwamnan ya yaba wa abokan karatunsa bisa yadda suke hade tare, yana mai cewa dangantakar ta taka muhimmiyar rawa wajen cusa kyawawan dabi’u a rayuwarsa.

Ya bayyana cewa,

“Haɗuwar ta kasance wani bikin tunawa da baya, soyayya da alaƙa ta musamman—rana ce da zan cigaba da tunawa a zuciyata har abada.”

Kara karanta wannan

"Za ku gane shayi ruwa ne," Gwamna ya fusata da ƴan bindiga suka kashe mutum 11

Dariyar da suka yi tare da tattaunawar soyayya ta nuna irin alaƙar da har yanzu ke cigaba da kasancewa a tsakanin su.

Buhari ya gana da abokan karatunsa a Daura

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da abokansa da suka yi rayuwa a baya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da 'yan ajinsu na makarantar firamare da sakandare a wata ziyara da suka kai masa a Daura.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng