"Carter Mai Son Cigabanmu ne," Tinubu Ya Yi Jimamin Mutuwar Tsohon Shugaban Amurka
- Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya mika ta'aziyya ga jama'ar Amurka bayan mutuwar tsohon shugabansu
- Jimmy Carter, wanda shi ne shugaban Amurka na 39 ya kwanta dama bayan ya shafe shekaru 100 a doron kasa
- Shugaba Tinubu, ta sanarwar da hadiminsa, Bayo Onanuga ya fitar ya bayyana yadda tsohon ya jagoranci ci gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana tsohon shugaban Amurka, Jimmy Carter, a matsayin aboki na hakika ga Najeriya da nahiyar Afrika.
Carter, wanda ya kasance Shugaban Amurka na 39, ya rasu a ranar Lahadi bayan cika shekaru 100 a duniya, amma ba a bayyana musabbabin mutuwarsa ba.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya wallafa a dandalin X, Tinubu ya mika ta'aziyyarsa ga gwamnatin Amurka da da al'ummarta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Jimmy Carter mai taimakon jama’a ne,” Tinubu
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Tinubu ya bayyana Shugaba Carter a matsayin fitila ta hidima ga bil’adama da ci gaban kasa.
Ya kara da cewa Carter ya nuna wa shugabanni a fadin duniya tasirin himma da jajircewa bayan rike babban matsayi duk da barin shugabancin Amurka.
“Shugaba Carter jagora ne a duniya,” in ji Tinubu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tuna da yadda tsohon shugaban Amurka, Jimmy Carter, ya jagoranci hanyar nuna wa shugabanni muhimmancin taimakon jama’a.
“Shugaba Carter ya nuna mana yadda za a kasance masu tasiri da amfani bayan barin matsayin shugaban Amurka,”
- Injji Shugaba Tinubu a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar.
Tinubu ya taya zababben shugaban Amurka murna
A baya, mun ruwaito cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya taya zababben shugaban Amurka, Donald Trump murnar nasara da ya yi a zaben kasar karo na biyu.
Tinubu ya bayyana fatan Trump zai jagoranci dawo da zaman lafiya a sassan duniya da ake samun rikici, tare da kara inganta kyakkyawar alaka da Najeriya domin ci gaba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng