Kwana Ya Kare: Mahaifiyar Sarki a Yobe Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

Kwana Ya Kare: Mahaifiyar Sarki a Yobe Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Sarkin masarautar Machina da ke jihar Yobe, Alhaji Dr Bashir Albishir Bukar Machina ya yi rashi mai daci a rayuwarsa
  • Mahaifiyarsa, Hauwa Mai Bukar ta riga mu gidan gaskiya bayan ta kwashe dogon lokaci tana yin jinya a fadar sarkin da ke garin Machina
  • Dubunnan mutane ne suka fito suka yi tururuwa wajen halartar jana'izar marigayiyar wacce ta samu shaiɗa ta halin kirki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Yobe - Mai Martaba Sarkin Machina a jihar Yobe, Alhaji Dr Bashir Albishir Bukar Machina, ya yi rashin mahaifiyarsa, mai suna Hajiya Hauwa Mai Bukar Machinawa.

Marigayiya Hauwa Mai Bukar ta rasu ne bayan doguwar jinya a fadar sarkin da ke garin Machina a jihar Yobe.

Mahaifiyar sarkin Machina ta rasu
Mahaifiyar Sarkin Machina ta rasu bayan ta yi jinya Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Mahaifiyar sarkin Machina ta rasu

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an gudanar da sallar jana'izar marigayiyar a fadar Masarautar Machina da misalin ƙarfe 11:00 na safe.

Kara karanta wannan

APC ta samu tagomashi, mataimakin shugaban majallisa ya tarbi 'yan adawa 3,000

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dubban mutane ne suka halarci sallar jana’izar marigayiyar wacce ta riga mu gidan gaskiya.

Marigayiyar ta samu shaida mai kyau

Ɗaya daga cikin jikokinta, Bukar Adamu, ya bayyana cewa ɗimbin jama’ar da suka halarci jana’izar, shaida ce kan girmamawa da ƙaunar da ta samu a tsawon rayuwarta.

Dr Kagu Abubakar, babban sakataren hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Yobe, wanda ɗaya ne daga cikin jikokin marigayiyar ya yi magana kan rasuwar.

"Ta yaye ni daga wajen mahaifiyata kuma ana yawan cewa ta shagwaɓa ni da soyayyar kaka."
"Tana kira na da Kwakori (laƙabin ta a gare ni). Lokacin da na haifi ƴata ta fari, na sa mata suna Hauwa.
"Mace ce mai kyawawan halaye. Allah ya sanya Aljannah ta zama makoma a gareta."

- Dr Kagu Abubakar

Ɗan gwamnan jihar Jigawa ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban ɗan gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ya yi bankwana da duniya a ranar Alhamis, 26 ga watan Disamban 2024.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi ram da mata da ke samar da makamai ga Bello Turji, an cafke dan acaba

Marigayi Abdulwahab Umar Namadi ya rasu ne sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya ritsa da shi a kan hanyar Dutse zuwa Kafin Hausa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng