Kamar dai Kullum: Gwamnatin Najeriya ta Gaza Cimma Burinta Kan Wutar Lantaki

Kamar dai Kullum: Gwamnatin Najeriya ta Gaza Cimma Burinta Kan Wutar Lantaki

  • Gwamnatin Najeriya ta gaza samun nasarar cimma burinta na tabbatar da wadatacciyar wutar lantarki ga ‘yan kasa
  • Wannan ya faru ne duba da wasu manyan dalilai da suka hada da sace kayan aiki da kuma lalata kayayyakin wuta a kasar
  • Sama da shekarun Najeriya 60 kenan da samun ‘yancin kai, amma har yanzu ba a samu damar samun wuta zaunanniya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Najeriya - Gwamnatin Najeriya ta kasa cimma burin samar da wutar lantarki mai karfin 6,000MW da aka tsara zuwa karshen 2024.

Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce lalata kayayyakin aikin wutar lantarki ne ya kawo cikas ga wannan tsari.

A halin yanzu, ana samar da wutar lantarki tsakanin 4,000MW zuwa 4,900MW a Najeriya, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Yadda wuta ta gaza zama a Najeriya a 2024
Wuta ta zama matsala a Najeriya a 2024 | Hoto: KEDCO
Asali: Facebook

Lalata kayayyakin aikin wuta na ci gaba da tada hankali

Ministan ya bayyana cewa, an samu ci gaba da Karin akalla megawatt 1,000 tun bayan karbar mulkin Tinubu, inda aka kai matsakaicin karfin 5,231MW a watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

An dauke wuta a babbar birnin tarayya Abuja, TCN ya fadi abin da ya jawo hakan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da haka, lalacewar turakun wutar lantarki ya yi matukar shafar ci gaban wannan fanni na samar da wutar lantarki.

An kashe N8.8bn kan gyaran turakun wuta

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya ya kashe N8.8bn domin gyaran turakun wutar lantarki 128 da aka lalata a fadin kasar.

Gwamnati ta tsara karin kudade a cikin kasafin 2025 domin inganta fannin wutar lantarki a shekarar da za a shiga nan da kwanaki.

A kasafin kudin 2025, za a ware N269.74bn don ayyuka na musamman, N47.35bn don gyara na’urorin wuta, da N36.82bn don samar da sabbin layukan wutar lantarki.

Akwai bukatar zuba hannun jari

Gwamnati na kokarin inganta yanayin da zai jawo kamfanoni masu zaman kansu su zuba jari a fannin wutar lantarki.

Ana kuma kokarin ganin an biya tallafin kudin wuta akan lokaci domin rage radadi ga ‘yan kasar a shekarar mai zuwa.

Najeriya na daga cikin kasashen da a duniya ke yawan fama da karancin wutar lantarki a tarihi, sama da shekaru 60 da samun ‘yancin kai.

Kara karanta wannan

NAFDAC ta kwace jabun kayayyaki na Naira biliyan 140, ta fadi yadda ta yi da su

An dauke wuta a babban birnin tarayya

A wani labarin kuma, kun ji yadda kamfanin wuta a Abuja ya sanar da cewa, zai yi gyara na dan wani lokaci.

Wannan ne ya kai ga dauke wuta a babban birnin tarayya, inda ake gudanar da harkokin mulki a Najeriya.

Abuja na daga cikin biranen da ke rasa wutar lantarki duk da kasancewarta babban birnin tarayyar kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.