An Dauke Wuta a Babbar Birnin Tarayya Abuja, TCN Ya Fadi Abin da Ya Jawo Hakan
- TCN ya sanar da cewa zai yi wani aikin gyara da zai shafi samar da wutar lantarki a Gwagwalada da Kukwaba, Abuja
- Tashoshin da TCN zai yiwa 'yan gyaran sun hada da Gwagwalada da Kukwaba, wanda zai shafi yankuna Wuye da Life Camp
- Kamfanin ya nemi afuwar mazauna yankunan, yana mai cewa gyaran na da muhimmanci don inganta aikin wutar lantarkinsu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kamfanin wutar lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar cewa zai gudanar da gyara a wasu tashoshi da hakan zai shafi samar da wutar lantarki a wasu sassan Abuja.
A wata sanarwa da Ndidi Mbah, manajan harkokin jama’a na TCN ya fitar a ranar Asabar, ya ce injiniyoyinsu za su yi gyaran a tashoshin wutar lantarki biyu.
An dauke wuta a wasu sassan Abuja
Ndidi ya ce a ranar Asabar, 28 ga Disamba, 2024, daga karfe 9 na safe zuwa 1 na rana, za a gyara tashar wutar mai karfin 60MVA da ke Gwagwalada, inji rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin da ake wannan gyara, kamfanin Abuja DisCo ba zai iya samar da wuta ga abokan huldarsa a Gwagwalada da kewaye na tsawon awanni hudu ba.
Haka zalika, a ranar Lahadi, 29 ga Disamba, 2024, daga karfe 9 na safe zuwa 10 na dare, za a gyara tashar wutar 60MVA da ke a Kukwaba.
TCN ta roki afuwar al'ummar Abuja
Wannan gyaran da TCN zai yi zai shafi wutar lantarki a Wuye, EFCC, cibiyar kiwon lafiya ta tarayya (FMC), Coca-Cola, tashar jirgin kasa ta Idu, Citec da Life Camp.
TCN ta nemi afuwa ga duk wata matsala da wannan gyara zai iya haifarwa, musamman a wannan lokaci na bukukuwan karshen shekara.
A baya-bayan nan, TCN ta dage gyaran tashar wutar 150MVA a Gwagwalada, wanda aka tsara yi a ranar 14 zuwa 15 ga Disamba.
'Yan ta'adda sun lalata turken wutar lantarki
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu bata gari da ake zargin 'yan ta'adda ne sun lalata turken wutar lantarki na Lokoja-Gwagwalada.
An ce lalata turken wutar mai karfin 330kV, ya jawo an dauke wuta a wasu sassa na Abuja yayin da TCN ya ce injiniyoyinsa na aikin gyara.
Asali: Legit.ng