Gwamnan Bauchi Ya Yi Ta'aziyyar Rasuwar Iyalan Takwaransa na Jigawa, Ya Yi Addu'a
- Gwamnan jihar Bauchi ya nuna alhininsa kan rashin da gwamnan Jigawa ya yi na wasu daga cikin iyalansa
- Bala Mohammed ya kai ziyarar ta'aziyya ga Gwamna Umar Namadi kan rasuwar mahaifiyarsa da babban ɗansa
- Gwamna Bala ya yi addu'ar Allah ya jiƙan mamatan da Rahama ya kuma ba iyalansu haƙurin jure wannan rashin da aka yi musu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Jigawa - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed Abdulkadir ya kai ziyara ga takwaransa na jihar Jigawa, Malam Umar Namadi.
Gwamna Bala ya kai ziyarar ne domin ta'aziyyar rasuwar mahaifiyarsa Hajiya Maryam Namadi Umar da babban ɗansa, Abdulwahab Umar Namadi.
Jaridar Tribune ta rahoto cewa Gwamna Bala Mohammed ya je ta'aziyyar ne a ranar Asabar, 28 ga watan Disamban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Iyalan Gwamna Namadi run rasu
Allah ya yi wa Hajiya Maryam Namadi Umar rasuwa a ranar 25 ga watan Disamba, 2024, bayan doguwar jinya a wani asibiti da ke Kano.
Yayin da babban ɗan gwamnan jihar Jigawa, Abdulwahab Umar Namadi, ya rasa ransa kwana guda bayan wani mummunan hatsarin mota.
Gwamna Bala ya yi ta'aziyya
A ziyarar da ya kai garin Gwamna Namadi da ke ƙaramar hukumar Kafin Hausa a jihar Jigawa, Bala Mohammed ya bayyana rasuwar a matsayin mai zafi amma ba ta da makawa kuma babbar jarrabawa ce ta imani.
Bala Mohammed ya lura da cewa mutanen da suka rasun sun kasance mutanen kirki waɗanda za a riƙa tunawa da irin gudunmawar da suke bayarwa ga al’ummarsu da iyalansu.
Ya yi addu’ar Allah ya jiƙansu da rahama da kuma ba iyalai haƙurin jure rashin wanda ba za a iya kwatantawa ba.
Da yake mayar da martani, Gwamna Umar Namadi ya yabawa Gwamna Bala bisa ziyarar ta'aziyyar da ya kai masa, sannan ya yi addu'ar Allah ya saka masa da alheri.
Buhari ya yi wa gwamnan Jigawa ta'aziyya
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya nuna alhininsa ƙan rashin da aka yi wa gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi.
Muhammadu Buhari ya yi gwamnan ta'aziyya sannan ya buƙaci ya ɗauki rasuwar mahaifiyarsa da ta babban ɗansa a matsayin ƙaddara daga Allah Maɗaukakin Sarki.
Asali: Legit.ng