Jami'an DSS Sun Yi Kwanton Bauna kan 'Yan Bindiga, Sun Tura Tsageru Barzahu

Jami'an DSS Sun Yi Kwanton Bauna kan 'Yan Bindiga, Sun Tura Tsageru Barzahu

  • Jami'an hukumar tsaro ta DSS sun samu nasara kan ƴan bindiga a jihar Neja da ke yankin Arewa ta Tsakiya
  • A wani harin kwanton ɓauna da suka kai kan ƴan bindigan a daren ranar Juma'a, sun hallaƙa tantirai guda uku har lahira
  • Jami'an na DSS sun kuma ƙwato makamai daga hannun ragowar ƴan bindigan da suka fatattaka zuwa cikin daji

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Jami'an hukumar DSS sun hallaka riƙaƙƙun ƴan bindiga aƙalla guda uku a jihar Neja.

Jami'an na DSS sun sheƙe ƴan bindigan ne a Dogon Dawa da ke ƙaramar hukumar Mariga ta jihar Neja.

Jami'an DSS sun kashe 'yan bindiga a Neja
Jami'an DSS sun hallaka 'yan bindiga a jihar Neja Hoto: @OfficialDSSNG
Asali: Twitter

Jami'an DSS sun sheƙe ƴan bindiga

jaridar Vanguard ta rahoto cewa jami'an DSS sun samu nasarar ne a wani harin kwanton ɓauna da suka kai kan ƴan bindigan a daren ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Bayan kwanaki 3 Shettima ya yi magana kan iftila'in harin bam a Sokoto

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi sun bayyana cewa a yayin harin, wasu ƴan bindiga da dama sun tsere cikin daji ɗauke da raunukan harbin bindiga.

Jami’an na DSS kuma sun ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda uku da babura uku daga hannun ƴan bindigan da suka tsere.

Yadda jami'an DSS suka shirya harin

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa harin na ranar Juma’a ya samo asali ne sakamakon tattara bayanan sirri, na tsawon makonni da kuma nazarin sadarwa tsakanin ƴan bindigan da jami'an DSS suka yi.

"Wannan farmakin na ɗaya daga cikin ayyukan jajircewa da jami’an DSS suka gudanar a shiyyar Arewa maso Yamma da kuma Arewa ta Tsakiya, wanda ya kai ga hallaka ko kama wasu ƴan bindiga da ke addabar yankunan."
"Hukumar ta DSS ta kuma jagoranci gudanar da ayyuka da dama inda suka samu nasara a kan haramtacciyar ƙungiyar IPOB a yankin Kudu maso Gabas."

- Wata majiya

Jami'an DSS sun cafke ɗan gwagwarmaya

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace malamin addini, sun bukaci N75m

A baya rahoto ya zo cewa wani ɗan gwagwarmaya mai suna Zubair Zubair ya shuga hannun jami'an hukumar DSS a jihar Kano.

Jami'an na DSS sun cafke ɗan gwagwarmayar ne wanda ya yi suna wajen sukar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a Kano sannan suka tafi da shi zuwa Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng