Mummunar Gobarar Ta Tashi a Fitacciyar Kasuwa, Ta Kone Shaguna Masu Yawa
- Ƴan kasuwa masu ɗimbin yawa sun shiga jimami bayan gobara ta lalata shagunansu a jihar Nasarawa da ke yankin Arewa ta Tsakiya
- Mummunar gobarar wacce ta tashi a daren ranar Juma'a, ta lalata kayayyaki na miliyoyin naira a kasuwar Masaka da ke ƙaramar hukumar Kauru
- Hukumar kashe gobara ta jihar ta bayyana cewa tsaikon da motarsu ta samu ne ya sanya ba a kai ɗauki cikin gaggawa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Nasarawa - An samu tashin wata mummunar gobara a shahararriyar kasuwar Masaka da ke ƙaramar hukumar Kauru a jihar Nasarawa.
Mummunar gobarar ta lalata shaguna masu ɗimbin yawa waɗanda ba a bayyana adadinsu ba, tare da ƙone kayayyaki na miliyoyin Naira.
Jaridar The Punch ta rahoto cewa gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 11:45 na daren ranar Juma'a, 27 ga watan Disamban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda gobara ta yi ɓarna a Nasarawa
A cewar wani ganau, gobarar ta faro ne daga wani gidan wanka sannan ta kuma bazu zuwa wasu shaguna da ke cikin kasuwar.
An tattaro cewa shaguna masu yawa musamman a sassan da ake sayar da ababen da za su lalace da kuma kayan lantarki, gaba ɗaya gobarar ta cinye.
Ɗaya daga cikin ƴan kasuwar da shagonsu ya ƙone mai suna Musa Hudu ya bayyana cewa gobarar ta ruguza shirin faɗaɗa kasuwancinsa a watanni masu zuwa.
Wane bayani hukumomi suka yi kan lamarin?
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Nasarawa, Builder Ombogus-Joshua, ya ce tawagarsa ta samu kiran waya da ƙarfe 11:45 na daren ranar Juma’a.
Sai dai, ya koka kan yadda motarsu ta lalace, kuma babu wata mota da za ta kai ƴan kwana-kwana zuwa wurin da lamarin ya faru a kan lokaci, lamarin da ya kawo tsaiko wajen isowarsu.
*Ana ci gaba da bincike, kuma da zarar an kammala, za mu tantance ainihin adadin shagunan da suka lalace."
- Builder Ombogus-Joshua
Gobara ta laƙume shaguna
A wani labarin kuma,.kun ji cewa an samu tashin wata gobara a fitacciyar Yar Dole da ke cikin birnin Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
RaRahotanni sun bayyana cewa gobarar ta shafi wasu shaguna da ke kasuwar wacce ta yi fice wajen sayar da babura da kayayyakin gyara.
Asali: Legit.ng