Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamna Ya Rasu
- Shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar Kwara, Prince AbdulKadir Mahe ya riga mu gidan gaskiya yau Asabar, 28 ga Disamba
- Sakataren watsa labaran gwamnan jihar Kwara, Rafiu Ajakaye, ya tabbatar da rasuwar a wata sanarwa da ya fitar
- Gwamna AbdulRahman AbdulRazak ya yi jimamin wannan rashin, ya roki ƴan Kwara su fahimci halin da gwamnati ke ciki na jimami
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kwara - Shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Kwara, Prince AbdulKadir Mahe, ya rasu.
AbdulƘadir Mahe, Yarima a masarautar Ilorin kuma tsohon babbban sakatare, ya riga mu gidan gaskiya ne a safiyar ranar Asabar, 28 ga watan Disamba, 2024.

Source: Facebook
Leadership ta ruwaito cewa wata majiya mai tushe ta ce za a yi jana’izar marigayin a gidansa na Adewole Estate, Ilorin da karfe 4 na yammacin yau Asabar.

Kara karanta wannan
"Za a binciko dalili": Tsohon dogarin shugaban ƙasa a Najeriya ya rasu yana da shekara 54
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ma'aikatan gwamnatin Kwara ya rasu
An kuma tabbatar da labarin rasuwar Abdulkadir Mahe a wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran gwamnan Kwara, Rafiu Ajakaye.
“Ya rasu a safiyar yau, 28 ga Disamba, 2024, kamar yadda Allah ya kaddara. Za a yi jana'izar marigayin yau a gidansa da ke kan titin Moro, Estate Adewole, Ilorin, bayan sallar La'asar.
"Mai girma gwamna ya yi matukar alhinin rasuwar Yarima Abdulkadir Mahe, mutumin kirki, jagoran al'umma na gari, ma'aikacin gwamnati, kuma dattijon ƙasa," in ji Rafiu.
Gwamna AbdulRazak ya yi ta'aziyya
Gwamnan ya mika ta’aziyyarsa ga mai martaba sarkin Ilorin Alh. Ibrahim Sulu-Gambari, iyalan marigayin, hukumomin gwamnati, da majalisar zartarwa.
AbdulRazak ya ce:
"Muna rokon al'umma su fahimci halin da muke ciki na juyayi da alhinin wannan rashi na kusa a gwamnati."
"Muna addu'ar Allah ya karbi ibadunsa, ya sauwake masa hisabi, ya shigar da shi gidan Aljannar Firdausi, ya kuma kyautata makwancinsa."

Kara karanta wannan
Matawalle ya fadi shirinsu bayan iftila'in harin bam a Sokoto, ya ba da gudunmawar kudi
Tsohon ADC na Jonathan ya kwanta dama
Kun ji cewa Allah ya yi wa tsohon dogarin tsohon shugaban ƙasa, Moses Jituboh ya rasu yana da shekaru 54 a duniya.
Marigayin ya yi aiki da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan tun yana gwamnan jihar Bayelsa har ya zama lamba ɗaya a Najeriya.
Asali: Legit.ng