'Yan Ta'adda Sun Fara Amfani da Jirage Marasa Matuka, DHQ Tura Sako ga 'Yan Najeriya

'Yan Ta'adda Sun Fara Amfani da Jirage Marasa Matuka, DHQ Tura Sako ga 'Yan Najeriya

  • Ƴan ta'addan Boko Haram/ISWAP sun fara amfani da jirage marasa matuƙa suna kai hari kan sojoji
  • Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana cewa jirage marasa matuƙan ba ƙwararru ba ne na wasan yara ne
  • Ta buƙaci ƴan Najeriya da ka da su firgita domin amfani da jirage marasa matuƙa ba sabon abu ba ne a fagen daga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta yi magana yayin da ƴan ta'addan Boko Haram/ISWAP suka fara amfani da jirage marasa matuƙa.

DHQ ta bukaci 'yan Najeriya da ka da su firgita sakamakon amfani da jirage marasa matuka da ƴan ta'addan suka fara yi wajen kai hari a wuraren da sojoji suke.

DHQ ta kwantar da hankalin 'yan Najeriya
DHQ ta kwantar da hankalin 'yan Najeriya bayan 'yan ta'adda sun fara amfani da jirage marasa matuka Hoto: @DefenceInfo
Asali: Facebook

Daraktan kula da harkokin yada labarai na DHQ, Manjo Janar Edward Buba, ya bayyana hakan ya yi ganawa da manema labarai a ranar Juma'a, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari ana tsaka da bikin Kirsimeti, sun hallaka bayin Allah

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me DHQ ta ce kan ƴan ta'adda?

Edward Buba ya ce jiragen da ƴan ta’addan ke amfani da su ba na soja ba ne, don haka babu buƙatar a firgita, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Ya kwatanta jirage marasa matuƙan da "kayan wasa" da ƴan ta'adda ke amfani da su wajen muzgunawa sojoji ba domin kai musu hari ba.

"Ba na tunanin akwai buƙatar wani firgici game da amfani da jirage marasa matuƙa da ƴan ta'adda ke yi."

"Muna yaƙi ne da ƴan ta'adda da masu tayar da ƙayar baya a faɗin ƙasarmu kuma duk abin da kuke buƙatar sani bai wuce da abin da kuke gani yana faruwa a Ukraine, Rasha, Isra'ila. Amfani da jirage marasa matuka a fagen daga ba sabon abu ba ne."
"Yanzu da muke magana game da jirage marasa matuƙa, don Allah ba ma son wata fargaba saboda waɗannan ba ƙwararru ba ne, ba jiragen sama marasa matuƙa na soja ba."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu zai yi jawabi ga 'yan Najeriya, ya sanya lokacin hirar farko

"Waɗannan kayan wasan yara ne da suka je siya suka sanya abubuwa ɗaya ko biyu a ciki domin su yi amfani da su. Suna da tasiri? Ba su da tasiri. Shin muna yin wani abu a kai? Eh muna yi."

- Manjo Janar Edward Buba

Sojoji sun cafke ɗan Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar cafke wani ɗan ta'addan Boko Haram a jihar Taraba.

Dakarun sojojin sun kuma cafke wani jami'in tsaro na ƴan banga wanda yake haɗa kai da masu garkuwa da mutane wajen sace mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel