Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Ya Ziyarci Gwamna domin Yi Masa Ta'aziyya

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Ya Ziyarci Gwamna domin Yi Masa Ta'aziyya

  • Sanata Ahmad Lawan ya je har gida yi wa gwamnan jihar Jigawa ta'aziyyar rasuwar mahaifiyarsa da ɗansa
  • Tsohon shugaban majalisar dattawan ya ce rashin ɗan uwa yana da ciwo balle kuma mutum ya rasa mahaifiya da matashin ɗa
  • Lawan ya yi wa gwamnan ta'aziyya a madadin mutanen Yobe ta Arewa, ya kuma roki Allah ya ba shi ƙarfin guiwar jure wannan rashi mai raɗaɗi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jigawa - Shugaban majalisar dattawa ta 9, Sanata Ahmad Lawan, ya kai ziyarar ta'aziyya ga gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi ranar Juma'a.

Sanata Ahmad Lawal ya je yi wa Gwamna Namadi ta'aziyya a gidan marigayya mahaifiyarsa da ke ƙaramar hukumar Kafin Hausa a Jigawa.

Ahmad Lawal da Umar Namadi.
Sanata Ahmad Lawan ya kai ziyarar ta'aziyya ga gwamnan Jigawa Hoto: Ahmad Ibrahim Lawan, Umar Namadi
Asali: Facebook

The Nation ta ce tsohon shugaban majalisar ya jajantawa gwamnan da iyalansa bisa rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Maryam da ɗansa, Abdulwahab Umar Namadi.

Kara karanta wannan

"Allah ya baku haƙuri," Shugaban APC Ganduje ya aika sako ga Gwamna Namadi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon shugaban majalisa ya ziyarci Namadi

Da yake jawabi, Sanata Lawan mai wakiltar Yobe ta Arewa a majalisar dattawa ta 10 ya ce:

"Ina matukar alhinin wannan rashi guda biyu, rasuwar ’yan uwa ba zato ba tsammani abu ne mai raɗaɗi, amma rashin uwa da ɗa a lokaci guda ya wuce duk yadda za a misalta.
"Rasuwar Hajiya Maryam babban rashi ne ga duk wanda ya santa, domin bayan kasancewarta Musulma mai kishin addini, tana ƙoƙarin tallafawa mutane.
“Dan gwamnan, Abdulwahab, mai shekaru 24, ya rasu a wani hatsarin mota a jiya, Alhamis, 26 ga Disamba, 2024, matashi ne mai tasowa. Rasuwarsa babban rashi ne ga iyalan Namadi da kasa baki daya."

- Ahmad Lawan.

Sanata Lawal ya yi wa gwamnan addu'a

Sanata ya miƙa sakon ta'aziyya ga gwamnan da iyalansa tare da addu'ar Allah ya ba su haƙurin jure wannan rashi.

“A madadin jama’ar mazaɓata da ‘yan uwana, ina addu’ar Allah SWT ya baiwa Gwamna Umar Namadi da iyalansa karfin gwiwa da juriyar wannan rashi," in ji shi.

Kara karanta wannan

Sakon Buhari ga Gwamna Namadi bayan rashin da ya yi, ya fadi abin da ya kamata ya yi

Shugaban APC, Ganduje ya yi wa Namadi ta'aziyya

A wani labarin, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya jajantawa gwamna Namadi bisa rasuwar mahaifiya da ɗansa.

Ganduje ya. ce rashin makusanta akwai ciwo da raɗaɗi, ya roki Allah ya jikansu ya sa Aljannar Firdausi ta zama makomarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262