"Za a Binciko Dalili": Tsohon Dogarin Shugaban Kasa a Najeriya Ya Rasu Yana da Shekara 54

"Za a Binciko Dalili": Tsohon Dogarin Shugaban Kasa a Najeriya Ya Rasu Yana da Shekara 54

  • Tsohon dogarin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan watau Moses Jituboh ya rasu ranar Juma'a a jihar Bayelsa
  • Moses Jituboh, tsohon mataimakin Sufeta Janar na ƴan sanda ya rasu ne bayan fama da gajeruwar jinya yana da shekara 54 a duniya
  • Marigayin dai ya koma aikinsa na ɗan sanda bayan Jonathan ya sha kaye a zaben shugaban kasa na 2015

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bayelsa - Tsohon dogarin shugaban ƙasa (ADC), Moses Jituboh ya riga mu gidan gaskiya ranar Juma'a, 27 ga watan Disambar 2024.

Moses Jituboh, dogarin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya mutu ne jiya bayan fama da gajeruwar jinya yana da shekara 54 a duniya.

Moses Jituboh.
Tsohon dogarin Jonathan ya riga mu gidan gakiya a Bayelsa Hoto: @DrEmekaKalu
Asali: Twitter

Wata majiya mai ƙarfi ce ta tabbatar da mutuwar tsohon ADC ga jaridar Punch amma ba ta bayyana abin da ya yi ajalinsa ba.

Kara karanta wannan

"Allah ya baku haƙuri," Shugaban APC Ganduje ya aika sako ga Gwamna Namadi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon ADC na Jonathan ya kwanta dama

Majiyar ta ce:

“Eh, bayanin da kuka samu gaskiya ne, ina tabbatar maku da cewa (Moses Jituboh) ya rasu. Yanzu na gama waya da shugaban yankinsu."
“A halin yanzu ana ci gaba da kokarin gudanar da binciken gawa don gano musabbabin mutuwarsa."

Jituboh ya yi aiki a matsayin dogari watau ADC na Jonathan lokacin yana gwamnan jihar Bayelsa da kuma lokacin da ya zama mataimakin shugaban kasa.

Ya ci gaba da zama a cikin tawagar tsaro ta Goodluck Jonathan bayan ya zama shugaban kasa.

Rundunar ƴan sanda ta yi ta'aziyya

Bayan zaben shugaban kasa na 2015 wanda Jonathan ya sha kaye, Jituboh ya koma bakin aikinsa a matsayinsa na ɗan sanda.

Tuni dai rundunar ‘yan sanda ta shiyya ta 16 ta jajanta wa dangin Jituboh da al'ummar jihar Bayelsa bisa mutuwar tsohon mataimakin Sufeto-Janar (DIG).

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na shiyyar, Emonena Gunn, ya fitar a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Rashin nadamar cire tallafin fetur da abubuwa 3 da Tinubu ya fada a kan manufofinsa

"Muna jajantawa 'yan uwa da mutanen jihar Bayelsa bisa rasuwar DIG Moses Ambakina Jituboh, mni," in ji sanarwar.

Tsohon AIG na ƴan sanda ya rasu

A wani labarin, kun ji cewa tsohon ƙaramin mataimakin babban sufetan ƴan sanda na ƙasa (AIG), Emmanuel Adebola Longe ya kwanta dama.

An ruwaito cewa marigayin dai ya yi abubuwan bajinta a yaƙi da ɓarayi wanda zai wahala a manta da shi a rundunar ƴan sanda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262