'Yan Sanda Sun Yi Bajinta, Sun Cafke Masu Laifi 859 a Jihar Arewa
- Rundunar ƴan sandan jihar Plateau ta yi bayani kan ƙoƙarin da jami'anta suka yi a shekarar 2024 da ke shirin ƙarewa nan da ƴan kwanaki kaɗan
- Kwamishinan ƴan sandan jihar, Emmanuel Adesina, ya bayyana cewa jami'an rundunar sun cafke waɗanda ake zargi mutum 859 tare da ƙwato makamai 27
- Emmanuel Adesina ya nuna cewa ƴan sandan sun samu waɗannan nasarorin ne sakamakon haɗin kan da jam'ar jihar suke ba su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Plateau - Rundunar ƴan sandan jihar Plateau ta bayyana nasarorin da ta samu a shekarar 2024.
Rundunar ƴan sandan ta ce ta kama mutane 859 da ake zargi, sannan ta ƙwato makamai 27 da alburusai 115 a jihar.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, Emmanuel Adesina, ya bayyana hakan a Jos a ranar Juma’a yayin wata ganawa da manema labarai, cewar rahoton jaridar The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan sanda sun samu nasara a Plateau
Adesina, wanda mataimakin kwamishinan ƴan sanda mai kula da ayyuka Nengi Jephthah ya wakilta, ya ce rundunar ta kuma ceto mutane 46 da aka yi garkuwa da su.
"Hakazalika, mun gurfanar da mutane 415 da ake zargi a gaban kotu bayan gudanar bincike a lokacin da ake bita a kai."
"A tsawon lokaci, mun samar da wasu tsare-tsare domin hana aikata laifuka da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama'a a jihar."
- Emmanuel Adesina
Adesina ya godewa gwamnatin Plateau da al’ummar jihar bisa goyon bayan da suke ba rundunar a yaƙin da take yi da aikata laifuka a jihar.
Ya ce nasarorin da ƴan sandan suka samu sun biyo bayan haɗin kai da goyon bayan da jama'a ke ba su, musamman a fannin bayanan sirri.
Ƴan sanda sun daƙile harin ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sanda sun samu nasarar daƙile wani hari da ƴan bindiga suka kai a jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yamma.
Ƴan bindigan dai sun kai harin ne a kan wata motar haya a titin Katsina zuwa Magama Jibia a ƙaramar hukumar Jibia ta jihar.
Asali: Legit.ng