NCAA: An Soke Tashin Jiragen Sama kusan 200 cikin Watanni 2 a Najeriya

NCAA: An Soke Tashin Jiragen Sama kusan 200 cikin Watanni 2 a Najeriya

  • Hukumar kula da harkokin sufurin jiragen sama watau NCAA ta koka kan ƙaruwar soke tashin jiragen sama a Najeriya
  • Muƙaddashin shugaban NCAA, Kyaftin Chris Najomo ya ce yana shan matsin lamba daga sama kan tsaikon tashin jiragen da ake samu
  • Ya ce a watan Satumba da Oktoba da suka gabata, an soke tashin jiragen sama 190 a sassa daban-daban na ƙasar nan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya (NCAA), ta nuna damuwa kan yadda ake samun ƙaruwar soke tashin jiragen sama a kasar nan.

Hukumar ta ce a watanni biyu kacal watau Satumba da Oktoba, an soke tashin jiragen sama daban-daban 190 a faɗin kasar nan.

Jirgin sama.
Hukumar NCAA ta bayyana damuwa kan karuwar soke tashin jiragen sama a Najeriya Hoto: Air Peace
Asali: Facebook

Daily Trust ta ce muƙaddashin darakta janar na NCAA, Kyaftin Chris Najomo ne ya faɗi hakan a wurin taron masu ruwa da tsaki a harkokin sufurin jiragen sama yau Juma'a.

Kara karanta wannan

Jihohin Najeriya sun yi kasafin sama da N74trn don magance talauci a 2025

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ake samun jinkiri da soke tashin jirgi

Ya ce a watan Satumba, an samu jinkirin tashin jirage 2,434 yayin da aka soke tashin 79 daga cikin sufurin jiragen sama 5,291 da aka tsara.

Najomo ya kara da cewa daga cikin jirage 5,513 da aka tsara tashinsu a watan Oktoban 2024, 2791 sun samu jinkiri yayin da aka soke tashin jirage 111.

Darakta Janar ya ce yana shan matsin lamba daga fadar shugaban kasa, Majalisar tarayya da ma'aikatar sufurin jiragen sama kan wannan lamarin.

Manya sun fara matsawa NCAA lamba

Kyaftin Chris Najomo ya ce:

"Shugaban Majalisar Dattawa ya kira ni ya na tambayar me muke yi ake samun wannan tsaiko da tangarɗa. A makon jiya kaɗai an samu jinkirin tashin jiragen sama da dama."

Shugaban NCAA ya ƙara da cewa duk da ya san ƙalubalen da kamfanonin sufurin ke fuskanta saboda ya yi aikin a baya, amma ba zai zauna ya zuba ido ana samun matsala ba.

Kara karanta wannan

Dangote ya fadi lakanin dake ruguzo da farashin man fetur a Najeriya, ya jero dalilai

"Samun jinkiri da soke tashin jiragen sama yana rusa tsare-tsare, asarar kudi da kuma ruguza kwarin guiwar da mutane ke da shi a kan hukumar sufurin," in ji shi.

Jirgin Air Peace ya samu tangarda a Abuja

A wani labarin, kun ji cewa wani jirgin saman kamfanin Air Peace ya samu tangarɗa yana dab da dashi daga Abuja zuwa jihar Legas.

Kamfanin sufurin jiragen sama na Air Peace ya ba kwastomomin da ke cikin jirgin hakuri, sannan ya samar masu da wani jirgin da kwashe su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262