An Kama Gawurtaccen Dan Daba Mai Kunna Riciki a Unguwannin Kano

An Kama Gawurtaccen Dan Daba Mai Kunna Riciki a Unguwannin Kano

  • Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kama wani matashi mai shekara 21 da ake zargi da jagorantar rikicin daba a unguwanni
  • Ana zargin matashin ya jagoranci tashin rikici a unguwanni kuma bincikensa da aka fara ya tono asirin wasu 'yan daba har an kama daya
  • Rundunar 'yan sanda ta bukaci hadin kan al'umma wajen bayar da bayanai domin magance rikice-rikice irin na daba a jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sanar da kama wani matashi mai suna Kabiru Jamilu a kan zargin hada rikicin daba a unguwannin Kofar Mata da Zango.

Matashin mai shekara 21 da aka fi sani da 'Awu', yana zaune a unguwar Zango kuma yana daga cikin wadanda ake zargi da hada rikicin daba wanda ya janyo damuwa ga mazauna yankin.

Kara karanta wannan

Lakurawa: Mazauna Kauyukan Sakkwato suka jawo muka jefa masu bam Inji Sojoji

Dan daba Awu
An kama 'yan daba a Kano. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa.
Asali: Facebook

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a Facebook cewa kama matashin ya biyo bayan bincike mai zurfi da kuma hadin kan al’umma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan daban Kano ya amsa laifinsa

Rundunar ta ce an kama Kabiru Jamilu ne a ranar 24 ga Disamba 2024, da misalin karfe 8:40 na dare, a kusa da Asibitin Murtala Muhammad.

Bayan kama shi, Kabiru ya amsa cewa shi ne ya jagoranci rikicin daba da ya barke tsakanin matasan Kofar Mata da Zango.

A yayin bincike, an kara samun wani mutum mai suna Umar Garba, mai shekaru 32, wanda aka kama dauke da wuka mai tsawo.

Za a gurfanar da 'yan daban da aka kama

Bayan kama su, an mika dukkansu zuwa sashen binciken manyan laifuffuka (CID) na rundunar domin gudanar da cikakken bincike.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike kan zarge-zargen da ake musu.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun dakile mummunan harin 'yan bindiga, sun ceto mutane da dama

Yan sanda sun bukaci hadin kan al'umma

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, CP Salman Dogo Garba, ya yi kira ga mazauna unguwannin Kofar Mata da Zango da su bayar da hadin kai ga 'yan sanda wajen magance rikicin daba.

Ya kuma bukaci al’umma su rika amfani da lambobin gaggawa na 'yan sanda ko kuma manhajar NPF Rescue Me domin sanar da abubuwan da ke faruwa a yankunansu.

Anambra: 'Yan sanda sun kama bam

A wani rahoton, kun ji cewa yan sanda sun yi hadaka da sauran jami'an tsaro wajen kai farmaki ga 'yan ta'adda a wata maboyarsu.

Rahotanni sun tabbatar da cewa jami'an tsaro sun yi nasarar wargaza ginin maboyar tare da kwato bama bamai 19 da sauran kayayyaki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng