Abba Kabir Yusuf Ya Yi Wa Gwamna Ta'aziyyar Rasuwar 'Dansa

Abba Kabir Yusuf Ya Yi Wa Gwamna Ta'aziyyar Rasuwar 'Dansa

  • An sake shiga jimami a jihar Jigawa bayan rasuwar yaron Gwamna Ahmed Umar Namadi kwana ɗaya bayan rasuwar mahaifiyarsa
  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusf ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga Gwamna Namadi kan rasuwar Abdulwahab Umar Namadi
  • Abdulwahab Umar Namadi ya rasu ne a ranar Alhamis, 26 ga watan Disamban 2025 sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya ritsa da shi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga gwamnan jihar Jigawa, Ahmed Umar Namadi.

Gwamna Abba ya miƙa saƙon ta'aziyyar ne ga Gwamna Namadi bisa rasuwar ɗansa, Abdulwahab Umar Namadi.

Gwamna Abba ya yi ta'aziyya
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi wa Gwamnan Jigawa ta'aziyyar rasuwar dansa Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Ta'aziyyar Gwamna Abba na cikin wata sanarwa ne da mai magana da yawun bakinsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdulwahab Umar Namadi ya rasa ransa ne a wani mummunan hatsarin mota a ranar Alhamis, 26 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

Mutuwa ta sake ratsa iyalan gwamnan Jigawa kwana 1 bayan rasuwar mahaifiyarsa

Rasuwarsa na zuwa ne kwana ɗaya bayan kakarsa kuma mahaifiya ga Gwamna Namadi ta rasu a ranar Laraba.

Gwamna Abba ya yi ta'aziyya

Gwamna Abba ya bayyana rashin a matsayin babban iftila'i, ba wai ga iyalan Gwamna Namadi kaɗai ba, har ma ga gwamnatin jihar Jigawa da ɗaukacin yankin Arewacin Najeriya.

Gwamnan na Kano ya yabawa marigayin bisa jajircewarsa kan ci gaban al’ummarsa, inda ya bayyana shi a matsayin matashi mai kyakkyawar gobe.

Abba Kabir Yusuf ya yi addu'ar Allah ya jiƙan mamacin Ya kuma ba iyalansa haƙurin jure wannan rashi.

"Wannan lokaci ne mai cike da jimami ga jihar Jigawa. Ina roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya sanya Abdulwahab a Jannatul Firdaus, Ya kuma ba Iyalan Namadi da al’ummar jihar Jigawa haƙuri a wannan lokaci na baƙin ciki."

- Abba Kabir Yusuf

Mahaifiyar gwamnan Jigawa ta rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Jigawa Ahmed Umar Namadi ya yi babban rashi a rayuwarsa bayan rasuwar mahaifiyarsa.

Hajiya Maryam Namadi ta rasu ne a ranar Laraba, 25 ga watan Disamban 2024 yayin da Gwamna Umar Namadi ba ya cikin ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng