"Mutanen da Suka Zaɓe Mu na Cikin Wahala," Gwamna Bala Ya Kara ba da Hakuri
- Gwamnan Bauchi ya nuna damuwa kan halin ƙuncin rayuwa da al'umma ke ciki bayan sun zaɓe su ne domin kawo sauyi mai amfani
- Sanata Bala Mohammed ya ce gwamnatinsa na iya bakin ƙoƙarinta wajen magance halin tsadar rayuwar da mutane ke ciki
- Gwamna Bala ya faɗi haka ne yayin da yake taya mabiya addinin kirista murnar kirismetin bana ranar Laraba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya bayyana damuwarsa kan yadda mutanen da suka zabe su ke fuskantar wahalar rayuwa.
Gwamna Bala ya ƙara bai wa al'ummar jihar Bauchi haƙuri tare da tabbatar masu da cewa gwamnatinsa na aiki tuƙuru wajen rage ƙuncin rayuwar da ake ciki.
Bala Muhammed ya bayyana hakan ne a cikin sakon da ya fitar na taya mazauna Bauchi da ƴan Najeriya murnar kirismeti ranar Laraba, Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Bala ya kara ba al'umma haƙuri
"Ina kira gare ku duka da ku ci gaba da yin hakuri, yayin da muke kokarin kawo karshen wannan matsin tattalin arzikin da ake ciki," in ji Bala Mohammed.
Da yake taya kiristoci nurnar kirismeti, gwamnan ya ce gwamnatinsa ta damu matuƙa da halin kuncin tattalin arzikin da al’ummar Najeriya ke ciki a halin yanzu.
Bala Mohammed ya ce gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin al'umma sun samu sasssaucin wannan ƙuncin da suke fuskanta saboda tsadar rayuwa.
Gwamnan Bauchi ya tausayawa mutane
A cewarsa, abin da ciyo ganin mutanen da suka zaɓe su, suka ba su amana domin kawo sauyi a rayuwarsu, sun wayi gari cikin wahalhalun rayuwa.
"Tabbas mun damu sosai duba da mutanen da suka zaɓe mu domin mu aiwatar da tsare-tsaren da za su inganta rayuwarsu, suna fuskantar wahalar da ba za ta misaltu ba."
Gwamna Bala ya ce a matakin jiha, gwamnatinsa na yin duk mai yiwuwa don magance wahalhalun da ake fama da su da kuma samar da rayuwa mai walwala a Bauchi.
Gwamma Bala ya ba Tinubu shawarwari
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Bala ya buƙaci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ake haska majalisar zartaswarsa domin har yanzu akwai bara gurbi.
Gwamnan na jam'iyyar PDP ya ce har yanzu akwai masu hana ruwa gudu, waɗanda ke ɓata kokarin da shugaban ƙasa ke yi.
Asali: Legit.ng