"Mun Rasa Uwa Ta Gari," Abin da Abba Kabir Ya Ce bayan Rasuwar Mahaifiyar Gwamna
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya na daga cikin mutanen da su ka halarci jana'izar mahaifiyar gwamnan Jigawa
- Hajiya Maryam Namadi ta rasu a safiyar Laraba, wanda ya sa gwamna Abba ya jagoranci tawaga zuwa Jigawa a yammacin ranar
- Abba Kabir ya roki Allah ya yi mata rahama da aljanna madaukakiya, yayin da ya ke ba iyalanta hakurin wannan babban rashi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Jigawa - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya halarci jana’izar Hajiya Maryam Umar Namadi, mahaifiyar takwaransa na jihar Jigawa, Umar Namadi a garinsu na Kafin Hausa.
Hajiya Maryam ta rasu ne a safiyar ranar Laraba, inda aka yi jana’izarta a yammacin wannan rana ba tare da jiran gwamnan da ke ziyarar aiki kasar waje ba.
A sakon da darakta janar na gwamna Abba a kan yada labarai, Sanusi Bature Dawakin, ya fitar a shafinsa na Facebook, ya ce rasuwar ta girgiza gwamnan Kano matuka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Kano ya yi ta’aziyya ga Namadi
A sakon da aka wallafa a shafin Facebook din Abba Kabir Yusuf, gwamnan ya mika ta’aziyyarsa ga daukacin iyalan gwamna Umar Namadi bisa babban rashin.
Gwamna Yusuf ya bayyana Hajiya Maryam a matsayin uwa mai kula da jin dadin al’umma wacce ta sadaukar da rayuwarta wajen taimakon bil’adama.
Gwamnan Kano ya nemawa Hajiya Maryam rahama
Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya sanya Hajiya Maryam a cikin Aljanna madaukakiya tare da bai wa iyalanta hakurin jure wannan babban rashi.
Gwamnan ya jagoranci wasu jami’an gwamnati zuwa Kafin Hausa, inda su ka halarci jana’izar marigayiyar kamar yadda addinin Musulunci ya shardanta.
Gwamnan Jigawa ya aurar da 'yarsa
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Jigawa, Umar Namadi ya aurar da 'yar sa, Dakta Salama Umar Namadi, inda tsofaffin jagorori a matakai daban-daban a kasar nan su ka halarta.
Daga cikin manyan mutane da suka halarci bikin auren akwai gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da na Zamfara, Dauda Lawal da Gombe, Inuwa Yahaya da na Katsina, Dikko Umaru Radda.
Asali: Legit.ng