Gwamna Ya Ziyarci Kauyuka 2 da Jirgin Sojoji Ya Jefa Bama Bamai kan Bayin Allah
- Gwamna Ahmed Aliyu ya kai ziyarar ta'aziyya kauyukan da ake zargin sojoji sun yi kuskuren jefa bama-bamai kan fararen hula a Sakkwato
- Gwamnan ya jajantawa iyalan mutum 10 da suka rasu tare da ba da tallafin Naira miliyan 20 domin su rage raɗaɗin rashin ƴan uwansu
- An ruwaito cewa jirgin yakin sojoji ya yi luguden wuta a wasu kauyuka biyu bisa kuskure, lamarin da ya jawo rasa rayuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto - Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya ziyarci garuruwa biyu da jiragen yakin sojoji suka yi musu luguden bama-bamai bisa kuskure.
Akalla mutane 10 ne suka mutu tare da jikkata wasu da dama a wani hari ta sama da ake zargin sojoji sun kai kan fararen hula a safiyar yau Laraba.
Gwamna Ahmed Aliyu ya kai ziyarar ta'aziyya
Sakamakon damuwar da ya yi da lamarin, Gwamna Aliyu ya tsallake duk wasu ƙalubale na rashin kyaun hanya, ya ziyarci kauyukan, cewar rahoton Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna ya kuma shiga cikin mutanen kauyen, an yi wa waɗanda suka mutu sallar jana'iza tare da shi.
Ya kuma ba da tallafin Naira miliyan 20 domin a rabawa iyalan waɗanda wannan ibtila'i ya afka mawa.
Ya samu rakiyar shugaban jam’iyyar APC a jihar, Sanata Aliyu Wamakko da ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Muhammadu Maigari Dingyadi.
Gwamnatin Sakkwato ta amince kuskure ne
Gwamna ya ce:
"Jiragen yaƙin soji na kan aikinsu ne na kawar da miyagu da kungiyoyin ƴan tada kayar baya, kwatsam suka yi kuskuren jefa bama-bamai kan fararen hula.
"Mun dauki wannan a matsayin kuskure ne saboda a lokuta da dama sojoji sun yi nasarar kai samame maboyar ‘yan ta’adda a jihar.”
"Za mu yi bincike kan lamarin" - Ahmed Aliyu
Ahmed Aliyu ya bayyana cewa za a gudanar da cikakken bincike domin gano abin da ya kai ga kuskuren domin a kiyaye afkuwar lamarin a gaba.
Ya kuma roki Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta wa wadanda suka rasu, ya kuma bai wa iyalansu hakuri da juriya.
Sojoji sun yi maganakan abin da ya faru
A wani labarin, kun ji cewa rundunar sojojin Najeriya ta ce wurin da ta jefa bama-banai a jihar Sakkwato yana da alaka da ƴan ta'addan Lakurawa.
Rundunar Operation Fansar Yamma ta yi kira ga ƴan Najeriya su rika tantance labaran da za su yarda da su, sannan su kaucewa yaɗa raɗe-raɗin da zai tada hankula.
Asali: Legit.ng