Rundunar Sojin Najeriya Ta Yi Magana kan Batun Jefawa Mutane Bama Bamai a Sakkwato

Rundunar Sojin Najeriya Ta Yi Magana kan Batun Jefawa Mutane Bama Bamai a Sakkwato

  • Rundunar sojojin Operation Fansan Yamma ta ce babu wani kuskure da jirgin yaƙi ya yi na jefa bama-bamai kan fararen hula
  • Rundunar ta bayyana cewa jirgin ya kai samame ne kan wasu da ake zargin suna da alaƙa da ƴan ta'addan Lakurawa a jihar Sakkwato
  • Wannan dai na zuwa ne bayan rahoto ya cika kafafen watsa labarai cewa sojoji sun yi luguden wuta kan bayin Allah. a kauyuka 2

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto - Rundunar sojojin Operation Fansan Yamma da ke aiki a Arewa maso Yamma ta yi ƙarin haske kan raɗe-raɗin jefa bam kan fararen hula bisa kuskure a Sakkwato.

Rundunar ta roki jama'a su rika dogaro da sahihan labarai domin kaucewa yaɗa rahotanni da za su tada hankula game da ayyukan sojoji.

Jirgin sojoji.
Rundunar sojin Najeriya ta musanta batun kuskuren jefawa fararen hula bom a Sakkwato Hoto: Nigeria Air Force
Asali: Facebook

Kodinetan sashen yaɗa labarai na rundunar haɗin guiwa ta Operation Fansar Yamma, Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi ne ya faɗi hakan a wata sanarwa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ziyarci kauyuka 2 da jirgin sojoji ya jefa bama bamai kan bayin Allah

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun yi magana kan kisan fararen hula

The Nation ta ce sanarwar dai martani ne ga rahoton da ake yaɗawa cewa jirgin yaƙin sojoji ya jefa bama-bamai kan fararen hula a yankin ƙaramar hukumar Silame a Sokoto.

Kanal Abubakar ya bayyana cewa sojoji ba su fita aiki irin wannan ba tare da tattara sahihan bayanan sirri ba.

Ya jaddada cewa tattara bayanan sirri na da matuƙar muhimmanci musamman a yaki da ƙungiyar ƴan ta'adda kamar Lakurawa.

Abdullahi Abubakar ya ce sai da suka tabbatar da wuraren na da alaƙa da ƴan ta'addan Lakurawa sannan jirgi ya yi barin wuta a kansu.

"Ba mu yi kuskure ba" - Rundunar soji

"Wannan babban haɗari ne idan ƴan ta'adda za su yi amfani da midiya wajen yaɗa labaran ƙarya da za su dakushe nasarorin da sojoji suka samu."
"Haka ya sa dole ne jama'a su taka tsan-tsan kan rahotannin da ba su tabbata ba musamman game da yaki da ƴan tada kayar baya da ƴan fashin daji."

Kara karanta wannan

"Ku kara hakuri": Sanata ya rabawa mutanen mazaɓarsa buhunan shinkafa 11,000

Abubakar Abdullahi ya ce jirgin soji ya kai farmaki Gidan Sama da Rumtuwa ne bayan tabbatar da cewa suna da alaƙa da ƴan ta'addan Lakurawa.

Sojoji sun kashe kasurgumin ɗan bindiga

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun nasarar kashe wani kasurgumin ɗan bindiga, Aljan, wanda ya addabi mazauna Tsafe a Zamfara.

An ruwaito cewa Aljan ya fito ne daga jamhuriyar Nijar kuma daga aikin adaidaita sahu ya zama ɗan bindiga

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262