Yan Sanda Sun Kama Limami da Wasu Jami'an Coci kan Ibtila'in da Ya Afku a Abuja
- Yan sanda sun damƙe limamin coci da wasu jami'ai kan zargin hannu a turmutsitsin da ya faru a birnin tarayya Abuja
- Akalla mutane 10 ciki har da ƙananan yara ne suka mutu sakamakon turereniyar da ta auku a wurin rabon tallafin abinci a coci
- Mai magana da yawun ƴan sandan Abuja, Josephine Adeh ta ce babu dalilin da za a shirya babban taro irin haka ba tare da sanar da su ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta kama wani limamin coci da jami’an cocin Holy Trinity Catholic Church.
Ƴan sanda sun kama mutanen ne bisa zargin sakaci a turmutstsin da ya auku wurin rabon kayan abinci wanda ya yi sanadin rasa rayuka a Abuja.
Yan sanda sun fara bincike kan lamarin
‘Yan sanda sun ce suna gudanar da bincike kan turmutsitsin da ya faru a Abuja da kuma wasu guda biyu a jihohin Anambra da Oyo, Premium Times ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akalla mutane 10 ne suka mutu yayin rabon kayan abinci ga talakawa a wurin ajiyar motoci da ke harabar cocin a Abuja ranar Asabar, cewar Punch.
A wani sakon Kirsimeti, babban limamin cocin Katolika na Abuja, Ignatius Kaigama, ya yi Allah wadai da kama jami’an cocin, yana mai cewa hakan bai dace ba.
"Akalla dai za mu iya cewa wannan ba daidai ba ne, me zai sa a kama waɗannan mutanen?" in ji Kaigama.
Dalilin kama waɗanda suka shirya rabon abinci
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Abuja, Josephine Adeh, ta tabbatar da lamarin, ta ce an kama su ne saboda sakacin da suka yi a wurin shirya rabon.
“Ta ya ya za ku shirya taro mai girma ba tare da sanar da ‘yan sanda ba?
"An rasa rayuka 10 ciki har da yara, wasu da dama sun jikkata, shin wannan bai kai a kama su ba."
"Ba zan iya cewa an kama limamin coci ba sai dai idan yana da alaƙa ko da shi aka shirya taron," in ji Adeh.
Ƴan sanda sun daƙile harin garkuwa
A wani rahoton, kun ji cewa yan sanda sun daƙile harin garkuwa da mutane a jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
Dakarun sun kuma yi nasarar ceto duka mutanen da ƴan ta'addan suka yi yunƙurin garkuwa da su a titin Jibia.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng