Babban Malami a Arewa Ya Dura kan Gwamnati, Ya Ce Ita Ta Jawo Rasa Rayuka a Jihohi 3

Babban Malami a Arewa Ya Dura kan Gwamnati, Ya Ce Ita Ta Jawo Rasa Rayuka a Jihohi 3

  • Babban malamin cocin nan na Sakkwato, Mathew Kukah ya ce gwamnati ce silar ibtila'o'in da suka faru a Abuja, Ibadan da Anambra
  • Kukah ya bayyana cewa duk waɗannan abubuwa da suka faru har aka rasa rayuka sun samo asali ne daga gazawar gwamnatin tarayya
  • Ya ce matasa ba su iya shiga harkokin siyasa ne saboda rashin kuɗin da za su ɗauki ɗauyin takarar neman kujerar gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto - Fitaccen malamin addinin kiristan nan da ke Sakkwato, Bishof Mathew Hassan Kukah ya ce gwamnatin Najeriya ta gaza wajen magance yunwa.

Malamin ya bayyana cewa gazawar gwamnati ne silar rasa rayuka a wuraren rabon tallafin kayan abinci a Abuja, Anambra da kuma Ibadan watau Oyo.

Bishof Kukah.
Bishof Kukah ya ɗora laifin rayukan da aka rasa a wurin raba tallafin abinci kan gazawar gwamnatin Najeriya Hoto: Biship Mathew Kukah
Asali: UGC

Gwamnati ta gaza magance matsalar yunwa

Bishof Kukah ya bayyana hakan ne a cikin saƙon da ya aikewa kiristoci na taya murnar bikin kirismetin bana 2024, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

"Gwamnatin Tinubu ta gaza," Jigon APC ya amince sun ba ƴan Najeriya kunya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma nuna takaicin yadda har yanzu Najeriya ke tafiya cikin duhu duk da samun ‘yancin kai sama da shekaru 60 da suka gabata.

Bishof Kuka ya kara da cewa koma baya da rashin ci gaban Najeriya yana da nasaba da yadda ƙasar ta zabi bin hanya mai duhu maimakon haske.

Abin da ya hana Najeriya ci gaba

"Ku yi tunanin matakin da Najeriya za ta taka idan muka zabi haske maimakon duhu. Ƙabilanci, son zuciya da kwaɗayi sune abubuwan da suka hana kasarmu ci gaba.
"Har yazu ana fargabar kabilanci da addini su ne asalin abin da ake kallo wajen samun damammaki, nuna wariya shi ke kawo tashin hankali da fushi.
“Har yanzu ba mu iya aiwatar da abin da taken ƙasarmu ya faɗa ba, ya ce: duk da ƙabila da harshe na iya bambanta, mun ɗauki kanmu ƴan uwan juna. Bambance-bambance baiwa ce daga Allah, mu ɗauke shi makamin haɗa kan ƙasa."

Kara karanta wannan

Yadda gwamnatin Tinubu ta shirya rabon tallafin N25,000 ga magidanta miliyan 15

Dalilin da ke hana matasa shiga siyasa

Malamin cocin ya kuma taɓo abin da ke karyawa matasa guiwa su gaza shiga harkokin siyasa, kamar yadda Channels tv ta kawo.

Ya ce kudaden da ake kashewa wajen neman mukaman gwamnati a Najeriya shi ne babban cikas ga matasa a harkokin siyasa.

Gwamnatin tarayya ta ce babu ruwan manufofin Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta musanta zargin da ake cewa matakan da ta Bola Tinubu ya ɗauka ne ya jawo turereniya a wurin karɓar tallafi.

Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris ya bayyana cewa babu ruwan manufofin Tinubu da abin da ya faru, yana mai cewa akwai laifin masu shirya rabon.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262