An yi Kare Jini Biri Jini tsakanin 'Yan Sanda da 'Yan Bindiga

An yi Kare Jini Biri Jini tsakanin 'Yan Sanda da 'Yan Bindiga

  • 'Yan sanda biyu sun rasa rayukansu yayin musayar wuta da masu garkuwa da mutane a Jihar Imo
  • An kashe 'yan bindiga uku, an kama wasu biyu, tare da kwato bindigogi shida da motoci guda biyu
  • Hakan na zuwa ne yayin da aka gwabza kazamin fada tsakanin 'yan sanda da masu garkuwa da mutanen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Imo - Rundunar 'yan sanda ta Jihar Imo ta tabbatar da rasa jami'ai biyu yayin wani farmaki kan masu garkuwa da mutane a Orogwe, karamar hukumar Owerri ta Yamma.

Kakakin rundunar, SP Henry Okoye, ya ce jami'an sun gamu da ajalinsu ne sakamakon harbin bindiga da suka sha yayin musayar wuta da miyagun.

Yan sanda
'Yan sanda sun gwabza da 'yan bindiga a Imo. Hoto: Legit
Asali: Original

Premium Times ta wallafa cewa an kashe 'yan bindiga uku yayin farmakin kuma an kama wasu biyu.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun dakile mummunan harin 'yan bindiga, sun ceto mutane da dama

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kai farmaki kan 'yan bindiga

Rundunar 'yan sanda ta Jihar Imo, tare da hadin gwiwar sashin yaki da masu garkuwa da mutane, ta kai wani farmaki kan sansanin masu laifi a Orogwe.

SP Okoye ya bayyana cewa an gudanar da farmakin ne bayan samun cikakken bayanan sirri da bincike kan ayyukan 'yan ta'addar.

'Yan sanda sun kama bindigogi da motoci

A yayin farmakin, jami'an 'yan sanda sun kwato bindigogi shida kirar AK-47, alburusai 113, da bindiga ta gida, tare da motoci biyu, Mercedes Benz ML 350 da Hijet.

A cewar SP Okoye, an yi amfani da motocin wajen aikata laifuffuka da suka hada da garkuwa da mutane da sace dukiyoyi.

'Yan sanda za su cigaba da kokari a Imo

The Nation ta wallafa cewa rundunar 'yan sanda ta Jihar Imo ta nuna alhini kan asarar jami'anta biyu, tana mai yabawa sadaukarwar su wajen kare al'umma.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan sanda suka kama miyagu 30,313 da bindigogi 1,984 a 2024

SP Okoye ya tabbatar wa jama'a cewa rundunar za ta ci gaba da gudanar da sintiri da hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaro yayin bukukuwan karshen shekara.

'Yan sanda sun farmaki 'yan ta'adda a Anambra

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan sanda sun kai farmaki kan wata maboyar 'yan bindiga a wani kauye a jihar Anambra.

Legit ta rahoto cewa jami'an 'yan sanda sun kwato boma bomai da dama tare da wargaza gine ginen da ke maboyar 'yan ta'addar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng